✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga na neman N1bn kudin fansar daliban Kaduna

A makon da ya wuce ne maharan suka sace dalibai sama da 200 a Kaduna.

’Yan bindigar da suka sace dalibai kimanin 287 a kauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna, sun bukaci Naira biliyan daya a matsayin kundin fansarsu.

Aminiya ta ruwaito yadda ‘yan bindigar suka kira daya daga cikin iyayen daliban domin neman kudin fansa, tare da kafa sharadin biyan kudin cikin kwanaki 20.

Daya daga cikin shugabannin matasan yankin, Aminu Kuriga, wanda ya tabbatar da hakan, ya shaida wa Aminiya cewa mutanen kauyen sun damu matuka.

“Sun bayyana cewa suna wani waje a Arewacin Zamfara tare da yaran kuma dole sai mun biya biliyan daya kafin nan kwanaki 20 masu zuwa.

“Sun samu lambata ne ta hannun shugaban makarantar da suka sace, Abubakar Isah, wanda abokina ne tun kuruciya. Muna addu’ar Allah Ya kawo mana dauki kan wannan lamari,” in ji shi.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda ‘yan bindigar suka mamaye makarantar a safiyar ranar Alhamis din da ta gabata, inda suka yi awon gaba da dalibai da malaman makarantar.

Gwamnan Jihar Uba Sani, ya ziyarci al’ummar kauyen sa’o’i kadan bayan faruwar lamarin, ya kuma tabbatar wa da iyayen daliban cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa an ceto ‘ya’yansu cikin koshin lafiya.

Sai dai duk da wannan tabbaci na gwamnan, babu labarin ceto ko da yaro daya daga cikin daliban da aka sace, face ma sai aka sake hangen wasu mahara a kofar shiga makarantar kwanaki kadan bayan harin farko.

Kawo yanzu dai, gwamnatin Jihar Kaduna ba ta ce komai kayan bukatar kudin fansar da maharan suka yi ba.

A gefe guda kuwa, Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da sace daliban, amma ya bayar da tabbacin gwamnatin tarayya za ta yi duk mai yiwuwa domin ceto daliban.

Ya kuma umarci jami’an tsaro da su ceto daliban Kaduna da kuma daliban tsangaya na Jihar Sakkwato da ‘yan gudun hijira a Jihar Borno da ‘yan ta’adda suka sace a makon da ya wuce.