✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Awawa sun hallaka matashi a Agege

Al’ummar Kasuwar Ilepo sun wayi gari da alhinin mutuwar wani matashi da ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a kasuwar, matashin mai suna Mustafa Sakkwato wanda…

Al’ummar Kasuwar Ilepo sun wayi gari da alhinin mutuwar wani matashi da ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a kasuwar, matashin mai suna Mustafa Sakkwato wanda ke shirin komawa gida kwana guda  kafin tsagerun nan masu fashi da makami wadanda aka fi sani da ‘yan Awawa suka hallaka shi a dakinsa da ke a unguwar Markas a Agege,

Makwabciyar mamacin wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaidawa Aminiya cewa ‘yan Awawan sun dirar wa gidan nasu ne da misalin karfe 3 na dare, inda suka shiga daukacin dakunan gidan suka yi ta kwatar wayoyi da kudaden mutanen gidan, “su biyu suka shiga dakin marigayin sai suka yi masa magana, ya ce masu baya jin yarbanci, su yi masa turanci, ana haka sai dayansu ya fita daga dakin, nan kuma sai marigayin ya kama dayan da kokawa, ko da barawon da ya fita ya farga ana kokawa da dan’uwansa sai yasa bindiga ya harbe shi a kafada, daga nan sai marigayin ya rike kafar barawon yana cewa azo a cece shi, da dayan barawon ya ga haka sai ya sa wuka ya yanke shi a wuya suka gudu abin su,” in ji ta. 

Tuni dai aka yi jana’izar Marigayi Mustafa Sakkwato kamar yadda addinin musulumci ya tanadar, ya kuma sami kyakkyawar shaida daga abokan sana’ar tasa da sauran abokan arziki da makwaftansa. 

Su dai ‘yan Awawa wasu gungun miyagu ne da suka dade suna addabar al’ummar unguwar Agege da kewayenta da fashi da makami, abin da kuma yake kai su ga hallaka jama’a a yayin wannan ta’addanci.