✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa ke kawo kashi 90 na abincin da ake ci a Legas – Sanwo-Olu

Dan takarar Gwamnan Jihar Legas a karkashin Jam’iyyar APC Mista Babajide Sanwo-Olu, ya nanata muhinmmancin da al’ummar  Arewa mazauna jihar suke da ita, inda ya…

Dan takarar Gwamnan Jihar Legas a karkashin Jam’iyyar APC Mista Babajide Sanwo-Olu, ya nanata muhinmmancin da al’ummar  Arewa mazauna jihar suke da ita, inda ya ce bayan gudunmawar da suke bayarwa a siyasance, su ke kawo fiye da kashi 90 cikin 100 na kayan abincin da ake ci a jihar, don haka zai ba su kulawa ta musamman da zarar ya samu nasarar cin zave a jihar.

Mista Babajide Sanwo-Olu ya bayyana haka ne lokacin da wadansu daga cikin shugabannin ’yan Arewa mazauna Legas suka karrama shi da sarautar gargajiya ta Tafidan Legas inda  Mai taimaka masa Dokta Kadri Hamzat aka yi masa sarautar Turakin Legas lamarin da ya faru a karshen makon jiya a fadar daya daga cikin shugabannin ’yanArewa mazauna Legas Sarki Sani Kabiru.

Mista Babajide Sanwo-Olu ya sha alwashin yin nazari bisa kudiri da koken da ’yan Arewar suka shigar masa, ya ce yana sane da dimbin gudunmawar da ’yan Arewa mazauna Legas ke bayarwa a jihar kan zamantakewar al’ummar jihar baya ga dimbin gudunmawarsu a siyasance, “Zan duba koke-kokensu, zan kuma ba su kulawa” inji shi.

Sarki Sani Kabiru, wanda ya jagoranci nadin sarautar  ya shaida wa Aminiya cewa, sun karrama Sanwo-Olu da sarautar gargajiya ta ’yan Arewa ce lura da yadda ya rungumi ’yan Arewa mazauna jihar, “Duk da a siyasar baya an bai wa ’yan Arewa mazauna Legas mukamin siyasa inda aka bai wa dan mu Akitet Ahmad Kabir babban  mukami, dole ne mu yaba amma hakan bai isa ba lura da irin gudunmawar da muke bayarwa a siyasance don haka muna fatan samun fiye da haka a gwamnati mai zuwa,” inji shi.

Ya ce, ya yi korafi bisa yawan kamen da ake yi wa ’yan Arewa masu kananan sana’a a jihar wadanda suka hadar da masu tukin babur na  acava ko okada da masu tallar hajojinsu, ya ce ana kama ’yan Arewa a garkame su a gidajen kurkuku inda ake cin tararsu makudan kudi don haka ya yi kira ga dan takarar Gwamnan na APC da ya share musu hawayensu da zarar ya samu darewa karagar mulkin jihar. “Don haka muka ba shi rubutaccen kudiri na ’yan Arewa bayan mun ba shi sarauta,” inji shi.

Alhaji Ahmad Kabir Babban Sakatare a Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Legas ne ya jagoranci zuwan dan takarar fadar Sarki Sani Kabiru, kuma ya shaida wa Aminiya farin cikinsa kan karamcin da ’yan Arewar suka yi wa Sanwo-Olu. Ya ce, ’yan Arewa mazauna Legas suna ba da gagarumar  gudunmawa a siyasar jihar, “Kamar yadda alamu ke nunawa idan aka kafa sabuwar gwamnati  za mu samu alfanun siyasar Legas fiye da yadda muka samu a baya” inji shi.

Alhaji Nasiru Ibrahim Gulma daya daga cikin wadanda suka shaida nadin sarautar ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna Legas su kaurace wa abubuwan da za su rarraba kawunansu a siyasance, “Bai kamata a ce mu zamo ruwan kashe gobara ba, sai lokacin da ake son cin moriyar ake neman mu. Saboda haka mu hada kai ta yadda za mu samu cin gajiyar siyasar, ’ya’yanmu su amfana,  mu guji rarabuwa da duk wani abin da zai kawo mana koma-baya,”  inji shi. Shugaban ‘Yan Tumatir na Kasuwar Mil 12 ya rasu