✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Arewa 123 da aka tsare a Legas sun bukaci a biya su diyyar Naira biliyan 1

‘Yan ciranin nan 123 da jami’an kwamitin cika aiki na Legas (task force) suka kama a ranar Juma’ar da ta gabata sun shigar da karar…

‘Yan ciranin nan 123 da jami’an kwamitin cika aiki na Legas (task force) suka kama a ranar Juma’ar da ta gabata sun shigar da karar gwamnatin jihar inda suka bukaci a biya su diyyar Naira biliyan daya.

Daya daga cikin ‘yan ciranin da aka tsare Abdullahi Yakubu, ne ya shigar da karar a babbar kutun tarayya da ke zamanta a Legas inda ya bukaci gwamnatin jihar Legas da ta biya su diyyar Naira biliyan daya saboda cin zarafin su da aka yi a lokacin da ake tsare da su.

Sunayen wadanda aka yi karar da ke takardar koken mai lamba  FHC/L/CS/1519/19 sun hadar da kwamishinan ‘yan sandan Legas CP Zubairu Mu’azu, da na shugaban hukumar tsaro ta Legas taskfos Yinka Ebgeyemi da ofishin alkalin alkalan jihar.

Lauyan da ya jagorancin lauyoyin da suka tsayawa ‘yan ciranin 123 mai suna Abba Hikima, ya bayyana cewa kame ‘yan ciranin da gwamnatin jihar Legas tayi ya tauye ‘yancin su na walwala kamar yadda yake a sashe na 41 na kundin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne jami’an kwamitin na Legas tare da taimakon shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Ganiyu Kola Ogunjobi suka kame ‘yan ciranin su 123 da baburan su 48 a cikin babbar motar tirela suka shigo Legas daga jihar Jigawa, kafin daga bisa ni hukumar ‘yan sandan Legas ta sallame su a ranar Asabar, kwanaki guda bayan ta tantance su ta tabbatar ba masu laifi bane, sai dai har zuwa yanzu ba a basu baburan su ba.