✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan adawar Senegal sun tsayar da Sonko takarar shugaban kasa

Wakilai sun kada kuri’a a sassa 46 na kasar ta Senegal.

Babbar jam’iyyar adawa ta Senegal ta ayyana shugabanta Ousmane Sonko a matsayin dan takararta, a zaben shugaban kasa tare da watsi da tambayoyi game da cancantar sa.

A ranar Alhamis ne aka zabi Sonko a matsayin dan takarar jam’iyyar PASTEF-Patriots na zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024, in ji jam’iyyar a cikin wata sanarwa ga Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

Wakilai sun kada kuri’a a sassa 46 na kasar ta Senegal da kuma ’ya’yanta da ke zama a wasu kasashen waje, kuma babbar hukumar gudanarwar jam’iyyar ce ta tabbatar da sakamakon.

Ousmane Sonko ya samu karbuwa a tsakanin matasan Senegal da ke fama da rashin gamsuwa da gwamnati mai ci, ta hanyar yin kamfe mai zafi a kan shugaba Macky Sall, na nuna shi a matsayin mai cin hanci da rashawa kuma mai mulkin kama-karya.