✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan a-waren Ambazoniya da ke Kurosriba na cikin tsaka mai wuya

 A makon da ya gabata ’yan gudun hijirar kasar Kamaru da ke fafutukar son kafa kasar Ambazoniya da suka fara kwarara zuwa wasu daga cikin…

 A makon da ya gabata ’yan gudun hijirar kasar Kamaru da ke fafutukar son kafa kasar Ambazoniya da suka fara kwarara zuwa wasu daga cikin kananan hukumomin Jihar Kurosriba tun daga watan Oktoba zuwa Disambar bara, yawansu a lokacin ya fara ne da mutum 5,000 cikin watannin uku kacal har sai da yawansu ya kai kimanin dubu 25. Kamar yadda Darakta-Janar na hukumar bayar da agajin gaugawa ta Jihar Kurosriba, John Inaku ya shaida wa wakilinmu.

’Yan gudun hijirar da a iya kiransu da ’yan a waren Kamaru, suna zaune a kananan hukummin Akamkpa, Akpabuyo. Sauran su ne Birnin Kalaba, Kalaba ta kudu, Ikom, Boki, Obudu da kuma Etung, wadda taf i iyaka da kasar Kamaru.

’Yan gudun hijirar, kamar yadda wakilinmu ya binciko, suna zaune ne a gidajen ’yan uwa da abokan arziki, ba a sansani daya suke zaune ba. Sai kuma ga jandarmomin Kamaru sun rika kawo masu hari a inda suke makale, lamarin da wasu jama’a ke ganin idan ba a yi hattara ba zai iya zama yaki tsakanin kasashen biyu.

Tun da farko dai Jamhuriyar Kamaru ta zargi Najeriya cewa tana horas da ’yan a waren Ambazoniya a boye, yayin da wasu kuma ke zargin mika daya daga cikin shugabannin kungiyar ce ta Gwamnatin Najeriya ta kama ta kuma mika wa Kamaru ya haifar da zafin cece-kuce tsakanin kasashen biyu.

Aminiya ta ziyarci karamar Hukumar Etung, ta zanta da wasu daga cikinsu da ke zaune a garin Abokim Obi da kuma Agbokim Waterfalls. Regina Agbor wadda ta tsallako daga Nsasarati, kasar Kamaru ta bayyana wa wannan jarida yadda aka yi ta tsira daga cin zarafin jandarmomin Kamaru, halin da ake ciki ma har yanzu ba ta san inda ’yarta daya take ba. “Muna zaune lami lafiya sai muka fara jin harbe-harbe cikin dare, ni kuma ba na gida, ka san ba ni kadai ba ce wurin mijina, ina da kishiya. Wayewar gari ke da wuya sai jandarmomi suka rika korarmu, suna cewa kowa ya fita, ni kuma da na ji haka da ma ’ya’yana suna daki na kulle su. Na tunkari gida sai jandarmomi suka bi ni suna tambayata inda za ni, wani kuma yana cakumo ni, na ce ’ya’yana zan dauko a gida. Koma me za ku yi mani sai na je. Duk da na tsorata ko za su bi ni ciki su yi mani fyade, haka na fito na kwaso ragowar yara uku, babbar ce ban san inda ta yi ba. Nan inda ka same mu ’yan uwa da abokan arziki ne da muka hada harshe daya suka ba mu mafaka,” inji ta.

Shi kuwa Eniebong Jerome, makaho dan kimanin shekara 70 da haihuwa ya ce lokacin da abun ya faru, shi dai ya ji harbe-harben bindiga amma “ni ba gani nake yi ba, na ji mutane na ta gudu suna cewa kowa ya yi ta kansa. Ni da ba ido ina za ni? karshe su ne jandarmomin suka fitar da ni, suka kawo kan hanya suka ajiye. Daga bisani kuma iyalaina suka gano inda nake, suka kawo ni wajen surikina, wanda shi ne yake kula da mu, mu wajen 28 ne yake kula da mu, yake taimaka mana. Ni rokona ga gwamnatin Kamaru shi ne, a sasanta mu koma gida, nan zaman da muke muna a takure ne. Abinci ma ba don Allah Ya sa suna ba mu ba, da ba mu san yadda za mu kare ba,” inji shi.

Ita kuwa Nguma Therasi, wata budurwa ce da aka tarar tana sassara asuwaki. Da aka tambaye ta ko yaya rayuwa ta kasance masu kuma ta yaya take tallafa wa kanta, ganin cewa sun baro gida sai ta ce: “Zaune nake ba na sana’ar komai, wannan ma maganin zama haka ne nake taimaka wa mai aikin asuwaki. Da haka nake samun abin da zan ci.”

Aminiya ta zanta da Daraktan hukumar bayar da agajin gaugawa ta Jihar Kurosriba, John Inaku game da kokarin da suke yi wajen kula da ’yan gudun hijirar. “Duk matsalolin da suke kokawa a kai na rashin abinci ko magunguna, lokacin da suka zo, dan abin da ake da shi a gwamnatance shi aka yi amfani da shi wajen ba su abinci da makwanci. Lokacin yawansu mutum dubu 5 ne kafin karshen shekara suka kai yawan mutum dubu 25. Zancen an da muke yi da kai yanzu haka ana da sama da mutum dubu 33.  ’Yan gudun hijira da ba su a cikin kasafin kudin Gwanatin Kurosriba duk da hukumar kula da ’yan gudun hijira ita ma ta yi bakin kokari, har yanzu yawansu a kullum kusan karuwa yake yi.”

Da aka tambaye shi game da harin da jandarmomi suka kawo wa ’yan gudun hijirar, daraktan agajin ya ce masu bi ta ruwa ne suka gamu da haka, yanzu sun gwammace su yanki daji su shigo Najeriya.