Bankin Duniya ya ce yakin da ake yi a Ukraine ya sanya harsashen da aka yi na ci gaban da tattalin arzikin daukacin duniya zai samu zuwa karshen shekarar nan ya ci karo da koma baya.
Shugaban Bankin, David Malpass, ya ce kiyasin da bankin ya yi tun da farko ya fadi daga ci gaba na kashi 4.1 cikin 100, zuwa kashi 3.2.
Kazalika, ya ce inda yakin zai fi yi wa illa sun hada da nahiyar Turai da Tsakiyar Asiya wanda ya hada da Ukraine da Rasha da kuma kasashen da ke makwabtaka da su.
Bankin dai ya yi hasashen tattalin arzikin zai iya raguwa da kashi 4.1 cikin dari.
A cewar shugaban bankin, bayanin ya fito ne bayan wani agaji da aka yi kiyasi, wanda ya kai na kudi kimanin Dalar Amurka biliyan 170 ga kasashen da lamarin ya shafa a cikin wata 15.
Har wa yau, ya ce yakin ya kawo koma baya ga samar da danyen mai a duniya da Rasha ke yi, lamarin da ya sanya farashinsa yin tashin gwauron zabo kusan sau biyu a baya-bayan nan.