✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakin Sudan: Najeriya ta tura jirgin soji don kwaso ’yan kasarta

Jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da aka tura zai tafi kayan abinci domin ’yan Najeriyan da zai kwaso

Gwamnatin Sojin Najeriya ta tura jirgin yaki domin kwaso ’yan kasar da yaki ya ritsa da su a kasar Sudan.

Jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da aka tura zai tafi kayan abinci domin ’yan Najeriyan, wadanda ake sa ran zai kwaso su zuwa gidan bayan sun isa kasar Masar.

A cikin dare ne Hukumar Kula da ’Yan Najeriya da ke Kasashen Ketare ce ta sanar cewa, “Jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya samfurin C-130 na shirin tashi zuwa kasar Masar domin kwaso ’yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan.

“Jirgin zai je da taren abinci da ruwan sha da magunguna da sauransu.”

Wani bidiyo da hukumar ta sanya a shafinta na Twitter ya nuna yadda sojoji ke loda ruwan sha da wasu kayayyaki a cikin jirgi da dare.

Ana kyautata zargin jirgin ne zai kwaso ’yan Najeriyan idan suka isa birnin Alkahira na kasar Masar.

Sai dai kuma Aminiya ta ruwaito cewa ’yan Najeriya da aka kwashe daga Khartoum, babban birnin kasar Sudan, sun shafe kwana uku a kan iyakar kasar Masar da ke Aswan ba tare da samun izinin shiga kasar ta Masar ba.

Rahotanni sun nuna daga iyakar ta Aswan zuwa birnin Alkahira, tafiyar akalla awa 12 ne a mota.