✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yakamata ’yan Arewa su yi karatun ta natsu’

Shugaban kungiyar Zabi Sonka da Taimakon juna ta kasa reshen Jihar Bauchi ta yi kira ga ’yan Najeriya da su guje wa siyasar bambancin addini,…

Shugaban kungiyar Zabi Sonka da Taimakon juna ta kasa reshen Jihar Bauchi ta yi kira ga ’yan Najeriya da su guje wa siyasar bambancin addini, ko yanki da kuma kabilanci domin kada a koma gidan jiya.

Shugaban Malam Nura Fatara dan Tireda ya yi wannan kira ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Azare. Ya ce harkokin zabukan kasa sun kawo jiki wadda ya sa wasu al’ummomin ke kokarin ko ta halin kaka sai sun jefa abubuwan da zai iya kawo nakasu ga samun zabe mai inganci da dukkan al’ummar kasa zasu amince da shi.
Ya kara da cewa: “Kamata ya yi a halin da ake ciki a ce al’ummar kasa musamman ma yankin arewaci su yi karatun ta nutsu dangane da wannan zabe da ke tafe domin ganin an kaucewa fada wa gidan jiya, wanda hakan ba zai samu ba sai har an hada kai tare da kaucewa siyasar nuna bangaranci ko kuma bambancin addini, maimakon haka kamata ya yi a raja’a ga waye zai mulke mu cikin adalci in mun zabe shi, amma ba daga ina ko wace jam’iyya ya fito ba,” inji shi.
Ya kara da cewa ba wai hakan ya tsaya ga zaben wanda zai mulki kasar nan ko gwamanoni kawai ya tsaya ba hatta wakilan da za su wakilce mu a matakin kasa da jahohi ya kamata a duba cancantar mutum ba wai kawai batun daga wace jam’iyya ya fito ba domin kuwa akwai yiwuwar a samu mutane masu adalci a kowace jam’iyya, “amma bai fito daga jam’iyyar da galibin jama’a suka fi so ba,” inji shi.
Daga nan ya kuma roki al’umma da a bi harkokin zabukan da ke tafe sannu da hankali domin kaucewa shiga halin rudu ko kuma tashe-tashen hankula wadda babu abin da zai haifar ban da barazana ga ci gaban kasar nan. Ya ce: “Jama’a su kai zuciya nesa a duk yayin da aka yi zabe tare da rungumar kaddara ga magoya bayan ’yan takarar da suka fadi, yin hakan ne zai sa a samu zaman lafiya da yar da da juna a cikin kasar nan mai dauke da addinai da kabilu daban-daban,” inji shi.