Kwana daya bayan Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta tsunduma yajin aiki, takwararta ta Kwalejojin Ilimi (COEASU) ta yi barazanar bin sahunta.
A ranar Litinin ne dai malaman jami’o’in suka tsunduma yajin aikin gargadi na tsawon sati hudu, kan zargin da suke yi wa gwamnati na kin mutunta yarjejeniyoyin da suka cimma da ita a baya.
- Zaluncin ’yan kasuwa ne ke kawo tsadar man fetur – Masu ababen hawa
- Farashin kayayyaki ya sauka a Najeriya a watan Janairu – Hukumar Kididdiga
A cewar malaman kwalejojin ilimin, su ma nan da ’yan makonni masu zuwa za su kira taron Majalisar Zartarwarsu don tattauna yiwuwar tsunduma yajin aikin, matukar gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba.
Da yake yi wa ’yan jarida jawabi a Abuja ranar Talata, Shugaban COEASU, Smart Olugbeko, ya ce jan kafar da gwamnati ke yi wajen cika musu alkawuransu ya nuna karara ilimi ba ya cikin alkiblar gwamnati mai ci.
Ya ce daga cikin alkawuran, wadanda wasu tun na shekarar 2009 ne, akwai batun kakaba musu tsarin biyan albashi na IPPIS, da kin fitar da kudaden bunkasa kwalejojin da yawansu ya kai kusan Naira biliyan 15 da sauran batutuwa.
Ya ce, “Duk kokarin da kungiyarmu ta yi wajen ganin hakarmu ta cimma ruwa, ya ci tura.
“Kungiyarmu ta jima tana taka-tsantsan wajen shiga yajin aiki, amma alamu sun nuna shi ne kadai yaren da gwamnati ke fahimta, ba tattaunawa ba,” inji shi.
Kungiyar ta kuma nuna takaicinta kan yadda ta ce gwamnati ta yi shakulatin bangaro da kwalejojin, musamman ta bangaren ayyukan raya kasa, inda ta bar su da ’yan kudaden da ke lalitarsu.