Ministan Kwadago da Kyautatuwar Ayyuka, Sanata Chris Ngige, ya dora laifin rashin cim ma daidaito don kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a ke ci gaba da yi a kan kungiyarsu ta ASUU.
Ngige ya ce ASUU ce ke jan kafa dangane da tattaunawar sulhu da ake yi tsakaninta da Gwamnatin Tarayya wanda hakan ya sa har yanzu aka kasa cim ma daidaito.
- Shirye-shiryen Sallah: ’Yan kaji sun koka kan rashin ciniki a Kaduna
- Mataimakiyar Shugaban Amurka ta kamu da COVID-19
Ministan ya yi wadannan kalaman ne ta bakin Shugabar Sashen Yada Labarai na ma’aikatarsa, Patience Onuobia, a matsayin martani kan rade-raden da ke cewa Ngige ne silar rashin janye yajin aikin na ASUU.
Ya yi ikirarin cewa, yana bakin kokarinsa don ganin an janye yajin aikin amma ASUU na hana ruwa gudu.
Ya ce ASUU ta ki amincewa da wasu matakai da gwamnati ta gabatar mata wadanda ake ganin za su taimaka wajen cim ma maslaha amma ki, sai abin da take so za a yi.
Sama da wata biyu ke nan da ASUU ta tsunduma yajin aiki don neman cim ma bukatunta a wajen gwamnati.