Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya mika kansa ga Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC).
Tsohon kakakin, Yahaya Bello, Ohiare Michael, ya sanar cewa, Yahaya Bello ya samu rakiyar wasu manyan mutane zuwa hedikwatar EFCC da ke Abuja, kuma nan gaba za a sanar da abin da ya wakana a tsakanin tsohon gwamnan da hukumar.
A cewarsa, Yahaya Bello yanke shawarar mika kansa ga EFCC ne bayan tuntubar iyalansa da kungiyar lauyoyinsa da kuma abokan siyasa.
“Tsohon Gwamnan, wanda ke matukar mutunta doka da oda, ya nemi a bi masa hakkinsa ne kawai domin a tabbatar da bin doka da oda, in ji sanarwar manema labarai da ya fitar a Lokoja.
- Gwammoni sun ciyo bashin N446bn duk da karuwar kudaden FAAC
- Sojoji sun cafke masu safarar makamai a Filato
“Shari’ar tana gaban wata kotun da ke da hurumin sauraren ta, kuma Alhaji Yahaya Bello ya samu wakilcin lauyoyinsa a kowane lokaci.
“Yana da kyau a yanzu tsohon Gwamnan ya mutunta gayyatar da EFCC ta yi masa na wanke sunansa saboda ba abin da zai boye kuma ba abin tsoro.
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna fatan hukumar EFCC za ta kasance mai nuna kwarewa kamar yadda ya kamata, tare da mutunta hakkinsa na asali a matsayinsa na dan Najeriya.”
Idan dai za a iya tunawa, tsohon gwamnan ya shafe watanni ana wasan bera da mage tsakaninsa da jami’an EFCC kan zargin sa da karkatar da biliyoyin kudade a lokacin da yake ofis a masayin gwamnan Jihar Kogi.