✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zaben Ghana ya gudana

A shekaranjiya Laraba ne al’ummar kasar Ghana suka fito kwansu da kwarkwatansu don kada kuri’unsu a babban zaben kasar. An bude rumfunan zabe, bayan da…

A shekaranjiya Laraba ne al’ummar kasar Ghana suka fito kwansu da kwarkwatansu don kada kuri’unsu a babban zaben kasar.

An bude rumfunan zabe, bayan da ‘yan takarar shugabancin kasar su bakwai suka yi kira da a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Kuma ga alama jama’a sun amsa kiran, inda aka kammala zaben lami lafiya. Tun da misalin karfe 7:30 na safe agogon Ghana aka fara kada kuri’u a zaben.
Shugaban kasar John Dramani Mahama na jam`iyyar NDC da Nana Akufor Addo na jam`iyyar NPP na cikin `yan takara bakwai da ke neman shugabancin Ghana.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton, an fara kidayar kuri`un da aka kada a zaben shugaban kasa da na`yan majalisar dokoki.
An kada kuri’a ne a mazabu kusan dubu 29, inda mutum miliyan 15 suka yi rijista domin yin zaben.
Masu sharhi dai na ganin cewa fafatawar za ta yi zafi ne tsakanin John Mahama da fitaccen jagoran adawa Nana Akufo Addo.
Duka ‘yan takara bakwai na zaben sun yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya.
Sai dai wani magoyin bayan ‘yan adawa ya rasa ransa a lokacin wata tarzoma da ta biyo bayan yakin neman zabe.
Batun tabarbarewar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa su ne suka mamaye yakin neman zaben.
Za a gudanar da zagaye na biyu nan gaba a watan nan, idan babu wanda ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 a cikin manyan ‘yan takarar biyu.
Ba dai wannan ne karo na farko da Nana Akufo-Addo mai shekara 72 ke tsayawa takarar shugabancin kasar ba, karo na uku ke nan da yake neman kujerar.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewa idan har ya sha kaye a wannan karo, to hakan zai kawo karshen damawa da ake yi da shi a siyasar kasar saboda shekarunsa.
A bangare guda kuma idan har Shugaba Mahama ya fadi zaben, to shi ne zai zamo shugaban kasar na farko da ya yi wa’adin mulki sau daya a tarihin dimukradiyyar Ghana.
Idan kuma ya yi nasara, zai kafa tarihin zama shugaba na farko na farar hula da ya dade ya na mulki tun bayan da Ghana ta fara amfani da jam’iyyun siyasa daban-daban.
Mahama ya karasa sauran wa’adin mulkin marigayi John Atta Mills da ya rasu a shekarar 2012.
Zuwa yammancin gobe Asabar ne ake saran samun sakamakon zaben.