A ranar Litinin 28 ga watan Yuni, 2022 ne Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta fara gudanar da taron zaben dan takarar shugaban kasarta a zaben 2023.
Taron nan zuwa ne bayan wata ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi da kusoshin jam’iyyar da suka hada da tsoffin shugabanninta da masu ci da gwamnoni da zummar fitar da dan takarar jam’iyyar ta hanyar masalaha.
- ‘Matakin Gwamnonin Arewa zai iya kayar da APC a zaben Shugaban Kasa’
- Mun daina kai wa CBN ajiyar kayan zabe —INEC
Har zuwa ranar Lahadi, jajibirin taron, yunkurin jam’iyyar na samar da dan takara ta hanyar masalaha bai yiwu ba, duk da kokarin da shugabannin jam’iyyar da sauran masu fada-a-ji suka yi a kan shawarar ta Buhari.
Mutum 33 ne suka sayi fom a hankoronsu na samun tikitin jam’iyyar, gabanin zaben da zai kawo karshen wa’adin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na biyu a karkashin inuwar jam’iyyar.
Sai dai daga cikinsu mutum 13 ne Kwamitin Tantance ’Yan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC ya sahale wa zawarcin kujerar:
- Uban jam’iyyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas – Bola Tinubu
- Mataimakin Shugaban Kasa – Yemi Osinbajo
- Tsohon Ministan Sufuri – Chubuike Rotimi Amaechi
- Gwamnan Jihar Ekiti – Kayode Fayemi
- Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom – Godswill Akpabio
- Gwamnan Jihar Ebonyi – David Umahi
- Tsohon Ministan Ilimi – Chukwuemeka Nwajiuba
- Tsohon Gwamnan Jihar Ogun – Ibikunle Amosun
- Attajiri Tein Jack-Rich
- Christopher Onu
- Shugaban Majalisar Dattawa – Sanata Ahmad Lawan
- Gwamnan Jihar Jigawa – Muhammad Badaru Abubakar
- Gwamnan Jihar Kogi – Yahaya Bello
Zaben fidda dan takarar na APC ya zo da sabon salo, inda a jajibirinsa, Gwamnoni 10 daga Arewacin Najeriya suka sanar da goyon bayansu ga yankin Kudu a tararar.
Gwamnonin Arewan sun kuma yi kira da ’yan Arewa da ke zawarcin kujerar da su janye su bar wa takwarorinsu na yankin Kudu domin hadin kan jam’iyya da ma Najeriya.
Sun kuma bukaci gwamnonin yankin Kudu, wadanda suka yi na’am da karamcin nasu, da su yi amfani da damar wajen zabo kwakkwaran dan takara ta hanyar masalaha.
Gwamnonin Arewa da suka sanya hannu a takardar janyewar yankin su ne:
- Nasir El-Rufai – Jihar Kaduna
- Aminu Bello Masari – Jihr Katsina
- Abubakar Bello – Jihar Neja
- Abdullahi Sule – Jihar Nasarawa
- Babagana Zulum – Jihar Borno
- Inuwa Yahaya – Jihar Gombe
- Bello Matawalle – Jihar Zamfara
- Simon Lalong – Jihar Filato
- Umar Abdullahi Ganduje – Jihar Kano
- Atiku Bagudu – Jihar Kebbi
Sai kuma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.
Tuni dai gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru ya janye daga takarar.
Ta rikice a APC
Sai dai kuma, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda shi ma yake zawarcin tikitin, ya ce ra’ayi ne kawai wadancan gwamnonin suka bayyana, amma ba wajibi ba ne.
Ya ce hasali ma, irin wannan ra’ayin na iya kara kawo rabuwar kai da bangaranci da kablinaci a tsakanin ’yan Najeriya.
Hakazalika, majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa wankin hula ya kai dare a yunkurin samar da dan takara ta hanyar masalaha daga yankin Kudu.
Majiyoyin sun ce a yayin da ake wannan kokari bayan Shugaba Buhari ya bukaci gwamnoni su fito da dan takarar da zai kai jam’iyyar ga nasara a 2023, manyan masu neman takarar daga yankin Kudu irinsu Tinubu da Osinbajo sun fi so a fafata a akwatin zabe.
Aminiya ta gano cewa duk da cewa wadansu daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar ta APC daga yankin na Kudu na duba yiwuwar janyewa, bangaren Tinubu da bangaren Osinbajo ba su nuna alamar hakan ba.
Yadda zaben zai kasance
Idan har jam’iyyar ta kasa yin masalaha, to zababbun daliget ne za su kada kuri’a domin zabe aya da tsakuwa.
Zababbun daliget uku daga kowacce daga kananan hukumomin Najeriya 774 za su jefa kuri’a.