Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana dakatar da aikin tattara sakamakon zaben gwamna a Jihar Adamawa.
Cikin wata sanarwa da babban jami’inta kan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa, Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zabe na Jihar Adamawa – REC ya dauka na sanar da wanda ya lashe zabe haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi amfani da shi ba.
Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa ba.
Hukumar INEC ta gayyaci duka jami’anta da ke lura da zaben gwamna a Jihar Adamawa, su kama hanyar zuwa Abuja domin yin wani taron gaggawa.
Hukumar INEC ta gudanar da cikon zaben gwamnan Jihar Adamawa ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, bayan ta ayyana zaben da aka yi a makonnin da suka wuce a matsayin wanda bai kammala ba.
Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar PDP shi ne ke kan gaba bisa alkaluman da INEC ta sanar kawo yanzu, yayin da Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC take bi masa a yawan kuri’u.
Yadda lamarin ya yamutsa hazo
An wayi gari a Jihar Adamawa cikin wani yanayi na dakon sakamako da ruɗani.
Tun da farko dai INEC ta dage aikin tattara sakamakon zaben a ranar Asabar, bayan karbar sakamakon zaben cike-gibi da aka yi cikin wasu tashoshin zabe na kananan hukumomin jihar 20.
A ranar Asabar da daddare, jami’in sanar da sakamakon zabe, ya bayyana sakamakon da aka samu a kananan hukumomi guda goma.
Daga bisani kuma ya dage aikin karbar sakamakon zuwa karfe 11 na safe a ranar Lahadi.
Sai dai da misalin karfe 10 na safe, sai babban jami’in INEC wato REC Barista Hudu Ari, ya shiga zauren tattara sakamakon zaben a Yola tare da rakiyar wasu sun rufa masa baya, inda ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaben.
Bai dai yi bayani filla-filla na sakamakon da kowacce jam’iyya ta samu da kuma yadda aka ci zaben ba.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa yana gama bayyana nasarar Binani ya kama hanya filin tashi da saukar jirage zai bar gari.
Wannan matakin ya sa INEC ta ce aikin da jami’inta ya yi haramtacce ne.