✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ku sauya tsoffin kudadenku a CBN

CBN ya kuma sanar da hanyar da masu tsoffin takardun kudin za su bi domin kauce wa asarar su.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce tun ranar 10 ga watan Fabrairu, tsoffin takardun N1,000 da N500 da N200 suka daina aiki.

CBN ya kuma sanar da hanyar da masu tsoffin takardun kudin za su bi domin kauce wa asarar su.

CBN ya kuma fitar da hanar da masu tsoffin takardun kudin za su bi domin kauce wa asarar su.

Babban bankin ya ce masu tsoffin kudin da ke so su ajiye suna iya kaiwa rassansa da ke jihohi su ajiye.

Hanyoyin da za a bi su ne:

  1. Mutum ya shiga shafin intanet na CBN ya kirkiri code domin ajiye tsofin takardun kudinsa. Ko kuma ya je ofishin bankin ya karbi fom ya cike.
  2. Mutum ya je da katin shaidarsa kowane iri wanda aka aminta da shi a kasa.
  3. Za a ba shi takardar tela ya cike domin ajiye tsoffin takardun kudinsa.
  4. Za a fara ajiye kudin ne daga ranar 15 ga watan da muke ciki har zuwa 17.

Wannan na zuwan ne duk kuwa da cewa Kotun Koli ya dage aiwatar da wa’adin ranar 10 ga wata da Bankin ya bayar zuwa ranar 15 ga wata.