Wasu bankunan kasuwanci a Najeriya sun bayyana cewa tuni suka bude sashen kula da hadahadar canjin Dala da sauran kudaden kasashen waje a rassansu bayan umarnin hakan da suka samu daga Babban Bankin Najeriya (CBN).
A makon jiya ne CBN ya soke tsarinsa na ba da canjin Dala kai-tsaye ga ’yan canji, ya kuma sauya akalar tsarin zuwa ga bankuna.
Wasu kwastomomin banki sun tabbatar mana da samun sakonni daga bankunan cewa sun bude sashen canjin kudade a rassansu ga masu bukata.
Sakon da bankin Sterling ya aike wa kwastomominsa ya ce, “Muna sanar da ku cewa za ku iya ziyartar kowane reshenmu kai-tsaye inda jami’anmu masu kula da canjin kudaden kasashen waje ke a shirye domin biya bukatunku.”
Wata kwastomar bankin Guaranty Trust, Comfort Oche, ta nuna mana sakon da kamfanin GTCO, mai maki kula da bankin ya aiko mata cewa, “Mun ware bangare na musamman a dukkannin rassanmu domin bukatunku na canjin kudade.”
Sakon ya ce masu bukatar canjin kudin guzuri ko biyan kudin makaranta ko na asibiti a kasashen waje da dangoginsu za su samu a rassan bankin.
Sakon ya ce masu bukatar canji za su samu a ranar da suka nema, amma sai sun cika duk sharuda da takardun da ake bukata.
“Dole mai neman canjin kudaden kasashen waje ya zama yana da akalla shekara 18 da kuma lambar BVN”, da sauransu.
Bankin ya kuma ayyana canjin Dala 4,000 a matsayin mafi yawan kudin guzurin da zai ba wa kowane mai bukata.