✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki tsabtace fuskarki

Kamar yadda kowane sassan jikinmu ke bukatar a tsabta ce shi, to haka fuskarki take bukatar a tsabtace ta. Don haka, ya kamata ki ba…

Kamar yadda kowane sassan jikinmu ke bukatar a tsabta ce shi, to haka fuskarki take bukatar a tsabtace ta. Don haka, ya kamata ki ba fuskarki kulawa ta musamman. Yana da kyau ki ware wasu lokuta domin kulawa da fuskarki. Akwai abubuwa da dama wadanda suka kamata ki rika yi kullum domin samun fatar fuska mai kyalli da laushi da kuma tsabta.
·         Yana da kyau ki rika shan ruwa a kullum, kamar kofi 8 don wanke maikon fuska.
·         Ki rika barci na awa takwas ko goma kasancewar jikinki na bukatar hutu.
·         Ki rika motsa jiki na tsawon minti 30.
·         Ki rika shan ‘ya’yan itatuwa masu dauke da sinadaran bitamin A da C domin ki samu fata mai sheki.

Hadin tsabtace fatar fuska:
·         Kofi 1 na bakin shayi
·         Cokali 2 na garin shinkafa
·         Rabin cokali na zuma
Ki kwaba ruwan bakin shayi da garin shinkafa da kuma zuma har sai hadin ya yi kauri, sannan ki shafa a fuskarki. Ki bari na tsawon minti 20, sai dai kafin ki wanke wannan hadin da kika shafa, yana da kyau ki goga hadin a fuskarki sosai, yin  hakan na cire matacciyar fata a fuska. Daga nan sai ki wanke fuskarki da ruwan sanyi.
·         Za ki iya amfani da kurkum da tumatir domin gyaran fatar fuska
Bayan kin matse ruwan tumatir, sai ki kwaba kurkum din da shi, sannan ki shafa a fuskarki kullum safe da yamma. Bayan minti 30 sai ki wanke da ruwan dumi. Wannan hadin na kara wa fuska haske da kuma kyalli.