✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki samu farin hakori

Mallakar hakora farare shi ne burin kowace mace a duniyar nan. Na taba ganin wata mata da ba ta son bude bakinta saboda hakoranta na…

Mallakar hakora farare shi ne burin kowace mace a duniyar nan. Na taba ganin wata mata da ba ta son bude bakinta saboda hakoranta na dauke da cin zuma. Na tausaya mata, domin ko an yi abin dariya sai dai ta sanya hannu a bakinta kafin ta yi dariya. Wannan dalilin ya sa na kawo miki hanyar da za ki samu farin hakora ko da kuwa hakoranki na dauke da cin zuma.
Lemon tsami
Ta hanyar amfani da lemon tsami ko jus din lemon tsami za su taimaka miki wajen samun farin hakori. Lemon tsami na dauke da sindarin acid mai karfi da zai wanke miki hakorinki ya yi haske da kuma fari.
Dokta Roth wani likitan hakori ne ya ce, kamar yadda ruwan lemon tsami ko jus din lemon tsami ke rina gashi, to haka suke sanya hakori ya yi fari.
Idan kika samu lemon tsami sai ki yanka shi, daga nan sai ki rika goshe hakorinki da shi, za ki yi hakan kamar tsawon minti uku ko hudu.
Idan kuma za ki yi amfanin da jus din lemon tsami ne, sai ki zuba jus din kamar cokali biyu, sannan ki gauraya shi da ruwa cokali biyu, sannan ki goge hakorinki da ruwan ta hanyar amfani da auduga.
Ba a so ki yi amfani da ruwan lemon tsami ko jus dinsa fiye da sau biyu a mako, domin lemon tsami na dauke da sinadarin acid da zai iya haifar da rubewar dadashi, kasancewar yana dauke da sinadarin da ke rage sinadarin calcium a hakori, wanda rashin wannan sinadari sai ya rage karfin hakori da dadashi.