✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki rabu da amosanin ka 1

Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata.…

Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. Wasu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ‘yan’uwa! Yau mun kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da wannan matsalar amosanin kai. A ciki akwai ganyen kashu da lemon tsami da ruwan kwakwa da kuma kwallon mangoro.

Shin ko kun san cewa ganyen kashu na maganin amosanin ka? To, ga yadda za a sarrafa shi.
•A wanke ganyen kashu sannan sai a daka shi a kwaba da ruwa.
•Bayan hakan, sai a shafa a fatar kai a bari na tsawon rabin awa kafin a wanke. Za a iya yin haka har na tsawon sati biyu in sha Allah za a sami saukin amosanin ka.
Ko kun san cewa lemon tsami ma yana warkar da amosanin ka? Musamman idan an hada shi da ruwan kwakwa.
•A sami lemon tsami sannan sai a matse ruwan, sannan sai a hada shi da ruwan kwakwa.
•Sannan a shafa a fatar ka a jira na tsawon rabin awa kafin a wanke.
kwallon mangoro yana mangance amosanin ka. Kuma ana iya hada shi ne da madarar ‘butter milk’ kamar haka;
•A busar da kwallon mangoro, bayan ya bushe, sannan a daka.
•Za a iya kwaba wannan garin kwallon mangoro da ruwa sannan a shafa a kai ko kuma da madarar ‘butter milk’ sannan a shafa a fatar kai .Bayan mintuna 30 sai a wanke. Ana yi akai-akai domin harkar fata sai a hankali ake samun sauki.