✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki magance fitowar gemu

Assalamu alaikum, barka da warhaka. Gemu na daya daga cikin abubuwan da ke bata kwalliya, inda duk hoda da fandeshi da mace ta sanya ba…

Man da ke fitar da gashiAssalamu alaikum, barka da warhaka. Gemu na daya daga cikin abubuwan da ke bata kwalliya, inda duk hoda da fandeshi da mace ta sanya ba za su kambama kwalliyar ba. Don haka ne a yau muka kawo miki hanya mafi sauki da za ki bi domin magance fitowar gemu a fuskarki.
·         Za ki iya magance fitowar gemu ta hanyar amfani da man cire gashin jiki, kamar (hair remobal cream), sannan ki jika auduga da ruwa, sannan ki goge wajen da kika cire gemun.
·         Za ki iya shafa kurkum bayan kin cire gashin gemu. Kurkum na hana alamar da ke nuna kin cire gashin gemunki.
·         Yana da kyawu ki kwaba kurkum da zuma, sannan ki shafa a fuska kafin ki kwanta barci. Yin hakan na kare fuska daga sake fitowar wani gashin.
·         Amfani da nikakken karas da nono ko madara na kara gyara inda gashin ya fito. Domin rabuwa da irin wannan matsalar ta hanya mai sauki, shawara a nan ita ce, kada ki yi amfani da wani man kanti ko wani sabulu, sai dai ki yi amfani da wadannan hanyoyin da muka yi bayani a sama.