✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki lura da sarkar gwal

Mata da yawa kan jin tsoro wajen yadda za su wanke sarkar gwal dinsu, tsoronsu shi ne ba sa so ta kode. Wannan dalilin ya…

Mata da yawa kan jin tsoro wajen yadda za su wanke sarkar gwal dinsu, tsoronsu shi ne ba sa so ta kode. Wannan dalilin ya sa na kawo miki yadda za ki lura da sarkar gwal dinki ba tare da tunanin kodewa ba.
Abubuwan da za a bukata:
. karamin kwano ko roba
. Sabulun wanke-wanke (Mild dish Detergent)
. Buroshin goge baki
. Tufafin da aka yi shi da auduga
. Tsumman da ake goge gwal
Matakan lura da sarkar gwal dinki:
Daga farko ki samu ruwan dumi (ba tafasshe ba), sai ki zuba shi a cikin karamin kwano ko roba, sannan ki zuba sabulun wanke-wanke da ake kira ‘mild dish detergent’ kadan, daga nan ki kada shi sosai, bayan nan ki sanya sarkar gwal dinki a ciki zuwa tsawon minti 20. Wannan zai babbago da dattin da ya makale a jikin sarkar. Shawara: Kada ki yi amfani man goge baki ko bakar hoda wajen wanke sarkar gwal dinki. Misalan sabulun wanke-wanken da za ki amfani da su sun hada da Smart da Meyers da Palm olibe da Dawn mild dish detergent.
Sai ki yi amfani da buroshi mai laushi, walau na goge baki ko wani, sannan ki rika goge sarkar da shi, Bayan nan ki dauraye ta da ruwa mai dumi, sannan ki goge ta da tsumman da aka yi da auduga. Kada ki yi amfani da takardar ‘tissue paper’ wajen goge sarkar gwal dinki, domin tana dauke da birbishin itatuwan da za su iya karje miki sarkarki.
Idan ta bushe sai ki goge ta da tsumman da ake goge sarka wanda ake kira ‘jewelry polishing cloth’, goge sarka da wannan tsumman zai sa ta rika kyalli da daukar ido.
Daga nan ki ajiye ta a wurin da kika saba ajiye sarkarki, idan ba ki da shi, to yana da kyawu ki tanadi akwatin musamman don ajiye sarkoki da ‘yan kunnenki.