✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki lura da fuskarki

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon mun kawo miki yadda za ki lura da fuskarki ta hanyar wanke fuska.…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon mun kawo miki yadda za ki lura da fuskarki ta hanyar wanke fuska. Muna fata za ki bi bayan daki-daki don kauce wa kuskure.

Me ya sa ya kamata a rika wanke fuska kafin a kwanta barci? Na san kowa zai so ya ji amsar wannan tambaya. Wanke fuska na da matukar muhimmanci ga mace da namiji. Mata da dama ba su damu da yin wanka da daddare kafin su kwanta barci ba. Wata ma tun kwalliyar da ta yi da daddare ta fita hira wajen saurayinta haka za ta shigo gida ta kwanta barci ba tare da ta wanke fuskarta ko kuma ta yi wanka ba. Don haka ya kamata ki canza, ki rika wanke fuskarki kafin ki kwanta barci saboda:
· Wanke fuska ko wanka kafin a kwanta na sanya kwanciyar hankali da samun barci mai dadi.
. Idan mutum ya kwanta ba tare da wanke fuska ba, mayukan da ya shafa a fuskarsa na taruwa su fitar da manyan kuraje, inda sai an yi da gaske kafin a rabu da su.
· Yana da kyau a wanke fuska da sabulun wanke fuska, domin fuska ba ta cika kwari ba kamar sauran fatar jiki.
· Kada a manta a rika goge fuska da sinadarin ‘cleanser’ kafin a kwanta barci.
· Ki yi amfani da ‘cleanser’ da ta dace da fatarki kafin a fara amfani da ita wajen wanke fuska.
· Rashin wanke fuska kafin a kwanta na rage wa mace kyau, domin idan kurajen suka feso a fuska kan samu matsala ko ta canza.
· Rashin yawan wanke fuska na janyo maruru a fuska.
· Rashin wanke fuska ko wanka na janyo fitowar kyasbi a fuska, don haka sai a kiyaye.