✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki gyara fuskarki a gida

Idan aka kira sunan mutum yakan yi amfani da fuskarsa wajen amsa kiran. Ya yarda fuskarsa ta wakilice shi, shi ya sa take daya daga…

Idan aka kira sunan mutum yakan yi amfani da fuskarsa wajen amsa kiran. Ya yarda fuskarsa ta wakilice shi, shi ya sa take daya daga cikin sassan jiki masu muhimmanci a gare shi. Don haka ya kamata mu san yadda za mu kula da fuskarmu ba tare da mun kashe kudi mai yawa wajen masu kwalliyar kanti ba. Akwai abubuwa da dama wadanda ba su kamata mace ta rasa su a gidanta domin gyara fuskarta ba. Yawan kwalliya da ado na kara soyayya a zukatan ma’aurata.
Abubuwan bukata:

·         Sabulun wanke fuska (face wash)

·         Dilke (Facial scrub)

·         Tawul

·         Man shafawa (moisturizer)

·         Zuma

·         Kurkum

·         Madara

·         Lemon tsami

·         Man essential oil ko zaitun

·         Ruwan rose (rose water)

Yadda za ki yi amfani da wadannan abubuwa wurin gyaran fuska:
·         Ki wanke fuskarki da sabulun wanke fuska, sannan sai ki wanke da ruwan sanyi.
·         Ki shafa dilke a fuskarki ta hanyar amfanin da tafin hannunki har na tsawon minti 2 kafin ki wanke da ruwan dumi.
·         Ki turara fuskarki da ruwan zafi na tsawo minti 5 bayan kin diga man zaitun ko man essential oil a cikin ruwan. Yin hakan zai cire miki bakaken kurajen fuska.
·          Sai ki hada madara da lemon tsami da zuma da ruwan rose water da kurkum kafin ki shafa a fuskarki har zuwa wuya. Daga nan ki bari na tsawon minti 15 ko 20 kafin ki wanke da ruwan dumi.
·        Daga nan ki goge da tawul kafin ki shafa man shafawa (moisturizer).
·         Ana so ki dinga yin hakan sau daya a sati domin samun fuska mai sheki kuma marar kuraje.