✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a yaƙi talauci a Arewa maso Gabas  — Shettima

NEDC ta ce shirin na ASSEP na da zummar inganta ilimin sakandare a yankin Arewa maso Gabas.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya buƙaci Hukumar Bunƙasa Arewa maso Gabas (NEDC) da ma’aikatar raya yankuna ta tarayya da su magance talauci a yankin ta hanyar zuba jari a fannin ilimi.

Shettima ya yi wannan kiran ne a yayin wata ganawa da ya yi da mahukuntan hukumar ta NEDC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda suka yi masa bayani kan wani shiri na harkokin ilimin babbar sakandare — ASSEP.

Ya kuma yaba wa hukumar NEDC kan yadda ta ke ba da gudummawar a fannin ilimi, inda ya ce za a riƙa tunawa da irin wannan ƙoƙari a nan gaba.

Shettima ya kuma yi nuni da cewa, akwai matsanancin talauci a yankin Arewa maso Gabas, inda ya kwatanta shi da wasu yankunan da ke fama da talauci a duniya, yana mai alakanta bullar ƙungiyoyin tsageru a yankin da irin waɗannan yanayi na zamantakewa.

Duk da kalubalen, ya yaba wa hukumar ta NEDC da abokan huldar ta, ciki har da Dokta Mariam Masha, saboda aikin da suke yi na inganta shirin ASSEP, yana mai cewa akwai yiwuwar canza yanayin yankin.

Mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci hukumar NEDC, ma’aikatar raya yankuna, da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai don samun ingantaccen aiki da samun nasara wajen aiwatar da shirin na ASSEP.

A nasa ɓangaren, Ƙaramin Ministan ci gaban yankin, Uba Ahmadu, ya lura cewa shirin na ASSEP na da zummar inganta ilimin sakandare a yankin, tare da ajandar Shugaba Bola Tinubu na inganta matakan ilimi na ƙasa.

Manajan Daraktan Hukumar NEDC, Alhaji Mohammed Alkali, ya yi cikakken bayanin dangane irin ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen bunƙasa rayuwar bil’adama, ciki har da horar da malamai da kafa cibiyoyin ilimin yanar gizo (ICT) a yankin.