✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a shimfida titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi

Layin dogon zai hade manyan garuruwa shida a Najeriya kafin ya keta Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar shimfida titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar a kan Dala biliyan 1.959.

A ranar Litinin Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar a madadin Najeriya, yayin da Manajan-Daraktan kamfanin Mota- Engil Group na kasar Jamus da aka ba wa aikin, Antonio Gvoea ya wakilci kamfanin.

Sanarwar da Daraktan Watsa Labaran Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Eric Ojiekwe, ta ce manufar aikin shi ne hade dukkannin sassan Najeriya da layin dogo.

Amaechi ya ce layin dogon da cibiyarsa za ta kasance a Arewacin Najeriya zai hade Jihohin Kano, Jigawa, da Katsina ya danga har zuwa Jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Ya kara da cewa kamfaninin zai kuma gina jami’a a Najeriya, a yayin da yake aikin, duk da cewa bai yi karin bayani a kan hakan ba.

Amaechi da Manajan Daraktan Kamfanin suna rattaba hannu kan yarjejeiyar.

Garuruwan da layin dogon zai keta sun hada Danbatta a Jihar Kano; Kazaure da Dutse a Jihar Jigawa; da kuma Katsina, Daura, Mashi, da Jibiya a Jihar Katsina.

Ministan ya ce titin jirgin kasar mai tsawon kilomita 283.750 zai taimaka wajen safarar mutane da dakon kaya, kuma za a sada shi da titunan muta.

Ya kara da cewa titin jirgin kasan zai taimaka gaya wajen habaka tattalin ariziki da bangaren zamantakewa a cikin gida.

Amaechi ya ce za a kammala aikin ne cikin shekara uku (wata 36) kuma ya kunshi tsarawa, sayo kaya da kuma gina layin dogon.

Mahalarta taron sanya hannun sun hada da Jakadan Najeriya a kasar Jamus, Yusuf Tuggar; da Manajan-Daraktar Hukumar Jiragen Ruwa ta Najeriya, Hadiza Bala-Usman; Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanin Mota-Engil Group, Mohammed Abdul-Razaq; da Daraktan kamfanin, Kola Abdulkarim.

Akwai kuma Magajin Garin Kano, Muhammad Wada; Babba Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Magdalene Ajani; Daraktan Harkokin Shari’a, Pius Oteh; da takwaransa na kamfanin Cameron Beverley; da Daraktan Kamfanin, Kola Abdulkarim.