✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a rabu da kaushin kafa

Tafin kafarmu na daya daga cikin sassan jikinmu da ya kamata mu rika kulawa da shi, kasancewar idan ba a yi hanzarin magance kaushin kafa…

Tafin kafarmu na daya daga cikin sassan jikinmu da ya kamata mu rika kulawa da shi, kasancewar idan ba a yi hanzarin magance kaushin kafa ba, sai ya zarce faso. Ta yaya za ki gane kina da kaushin kafa? A lokacin da kika fara jin tafin kafarki na janyo audugar jikin kujerar daki ko bargon da kike lullubuwa da shi, ko kuma yana kama kaya ko na gogar jikinki, idan kika ji haka to kina da kaushin kafa.
Mutane da dama na son rabuwa da wannan matsalar don haka ne muka kawo miki hanyoyi da za ki bi don rabuwa da kaushin kafa.
·         Ki zuba ruwan dumi a cikin bokiti ko wani abu mai fadi, sannan ki sanya kafarki a ciki.
·         Bayan tafin kafarki ya juku, sai ki cire daga ruwan dumin, daga nan ki dauki dutsen goge kafa, sannan ki rika goge tafin kafarki wurin da yake da kaushi. Ki rika zagaya dutsen a wuraren da kaushin ya fito, daga nan ki sake mayar da kafarki cikin ruwan dumi.
·         Bayan kamar minti 15 sai ki sake goge tafin kafarki da dutsen goge kafa domin cire fatar da ta mutu a tafin kafarki.
·         Daga nan ki wanke tafin kafarki da sabulu a cikin ruwa. Bayan nan sai ki cire kafarki, sannan ki goge da tawul.
·         Daga nan ki shafa man tafin kafa, idan ba ki da shi sai ki shafa man baseline.
Bayan nan sai ki sanya safa, sannan ki sanya kafarki a cikin leda, bayan ki daure sai ki kwanta barci. Ba za ki kwance ba sai washegari.