✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance warin gashin kai

Warin gashin kai na daya daga cikin abubuwan da ke tayar wa mata da dama hankali, sai a ga mace ta yi ado ta fita,…

Warin gashin kai na daya daga cikin abubuwan da ke tayar wa mata da dama hankali, sai a ga mace ta yi ado ta fita, amma ana jin wari. Ba wani abu ba ne illa warin da ke tashi daga gashinta, saboda matsalar fatar da kai wacce ke janyo warin gashi. Yawan sanya man gashi na kara haifar da warin gashi, musamman idan man ya yi yawa, kuma ya hadu da ruwa sai gashi ya fara wari. Yawan barin gashi ya yi datti sosai ma na janyo warin gashi.

· Idan za a sayi man wanke gashi (shampoo), to ya kamata a sayi wanda ke dauke da sinadarin sulphur ko zinc ko kuma mai kashe kwayoyin cuta (anti-bacterial).
· Man wanke gashin kai mai dauke da sinadarin silicyl na magance warin gashi.
· Za a iya amfani da lemon tsami domin magance warin gashi. Bayan an wanke gashin sai a matse lemon tsami a hada da ruwa sai a yi wa gashin wankin karshe.
· Ruwan tumatir na magance warin gashi. Kafin a wanke gashi da man wanke gashi, a matse ruwan tumatir sannan a shafa a fatar kai. A jira tsawon minti 10 kafin a wanke da man wanke gashi (shampoo).
· Ana iya hada ruwan ganyen dogon yaro a cikin man wanke gashi, sannan a gauraya su sosai kafin a fara amfani da shi, yin hakan na rage warin gashin kai.
· Za a iya samun man gashin kai da ke dauke da man labender domin samun kamshin gashi a kodayaushe.