✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance matsalar tsaro a Najeriya — IBB

Ba wai kawai a Najeriya ba, kasashe da dama sun gamu da irin wannan matsalar.

Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya shawarci Gwamnatin Tarayya a kan dabarun inganta tsaro a yayin da matsalar hakan ta yi wa kasar daurin dabaibayi.

Janar Babangida ya bukaci Gwamnatin da ta zage damtse wajen horar da sojoji tare da tanadar musu da kayan aiki na zamani domin dakile a matsayin babban lagon magance matsalar tsaro a kasar.

IBB yayin zantawarsa da manema labarai inda ya taya musulmi murnar bikin karamar sallah, ya bayyana damuwa matuka kan matsalar tsaro da ta addabi kasar, lamarin da ya ce har yanzu bai gushe ba wajen ci gaba tuntuba da shawartar gwamnatin a kan matsalar.

Sai dai ya ce tilas ne al’ummar kasar su bai wa gwamnati da dakarun tsaro hadin kai domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

“Ya zama wajibi ga ’yan kasa su tallafawa gwamnati da sojoji domin kawo karshen matsalar tsaro.

“Babbar gudunmuwar da jama’a za su bayar kenan daga nasu bangaren domin ganin an shawo kan matsalar da ta ki ta ki cinyewa” in ji shi.

Dangane da batun rawar da masu rike da madafan iko ke takawa wajen magance matsalar tsaro a kasar, tsohon shugaban na mulkin soja ya ce “akwai abubuwa da dama da ake bukatar su daidaita sannan su yi nazari a kai, na yi imani idan suka yi hakan za a cimma nasara.”

“Akwai bukatar a samar da sojoji duk abin da suke bukata sannan kuma a sanar da su tare da sanya musu akidar cewa wannan ita ce kasarsu, ba su da wata kasar da ta fi ta.

“Sojojin Najeriya na bukatar makamai na zamani sannan kuma suna bukatar a basu horo kan yadda za su yi amfani da makaman na zamani, ba wai kawai a sama musu makamai ba, ya kamata kuma a basu horo,” in ji shi.

“Wannan matsalar ta rashin tsaro, kowace gwamnati ta fuskance ta, amma idan muka hada kai, ina tuna yadda muka yi yakin basasa tsawon shekaru uku, kuma mutane suka goyi bayan gwamnati kuma ta yi iyaka bakin kokarinta wajen aiwatar da abin da ya dace.

“Haka kuma wadanda suka yi yakin aka sanya su fahimci cewa wannan kasar ce wurin da ya fi kowanne kyau a gare su.

“Ba wai kawai a Najeriya ba, kasashe da damu sun gamu da irin wannan matsalar, wasu sun yi fama da ita tsawon shekaru goma, amma ta hanyar hadin kai, sun futa daga cikinta.

“Na yi imanin za mu iya fita daga wannan matsalar idan duk shugabanni da wadanda ke jagoranta suka dage, amma ya kamata mu san cewa ba abu ba ne mai sauki.”