✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance karyewar gashi

Akwai abubuwa da dama wadanda ke janyo karyewa ko tsinkewar gashi wadanda da yawa daga cikinmu ba su san da su ba. Gashi na kara…

Akwai abubuwa da dama wadanda ke janyo karyewa ko tsinkewar gashi wadanda da yawa daga cikinmu ba su san da su ba. Gashi na kara wa mace kyawu, don haka ya zama dole mu lura da gashin kanmu sosai. Yau mun kawo muku abubuwan da ke kawo tsinkewar gashi domin a kiyaye da kuma yadda za a magance wadannan matsalolin.
·         Rashin sanya dankwali na janyo karyewar gashi, saboda idan rana ta haskaka shi sosai, hakan na sanya fatar kai ta zama marar karfi, sai ta fara zubar da gashi.
·         Yawan amfani da na’urar gasa gashi (dryer) domin busar da gashi na sanya karyewar gashi.
·         Damuwa da yawan tunani na janyo tsinkewar gashi.
·         Rashin cin abinci mai dauke da sinadaran bitamin da protein da sauransu, na sanya karyewar gashi, haka ma rashin amfani da man zaitun.
·         Gashin masu dauke da juna biyu na yawan tsinkewar saboda canjin da jikinsu ya samu.
·         Amfani da magunguna masu karfi saboda kyankyani da sauransu na janyo tsinkewar gashi, haka kuma yawan sanya man gashi a-kai-a-kai kamar ‘relader’ na janyo tsinkewar gashi. Ana so a rika amfani da man ‘relader’ bayan wata uku-uku.
·         Barin gashi ya yi datti sosai na janyo amosanin-ka da kuma karyewar gashi.
Yadda za a magance wadannan matsaloli:
·         Domin samun gashi mai lafiya da fatar kai mai karfi, sai a dage da shafa man gashi a fatar kai kamar man kwakwa da na zaitun da sauransu.
·         Domin rage furfurar gashi,yana da kyau a dinga shafa lalle a gashi bayan awa daya sai a wanke.
·         Idan ana so a rabu da amosanin-ka, sai a samu kwallon mangwaro bayan an shanya shi ya bushe, sai a rika hada shi da man gashi kafin a shafa a fatar kai.
·         Yana da kyau a rika wanke gashi da ruwan dumi, sannan sai a karshe a wanke da ruwan sanyi. Ruwan sanyi na kara karfin jijiyoyin da ke rike da gashi.
·         A dage da cin abinci mai dauke da sinadaran iron da zinc da B compled da bitamin C domin samun gashi mai santsi kuma mai lafiya.
·         A hada gwaiduwar cikin kwai da nono, sannan a shafa a gashi na sanya laushin gashi.
·         A hada lalle da kofi sai a shafa a kai, sanna a wanke bayan awa daya na magance furfura a gashi.