✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance gishirin hanci da kurajen kan hanci daga fesowa

Wannan matsalar ba mata kadai ta shafa ba domin wasu mazaje ma na fuskantar wadannan matsaloli. Bayan mutum ya yi gumin fuska idan wannan gumin…

Wannan matsalar ba mata kadai ta shafa ba domin wasu mazaje ma na fuskantar wadannan matsaloli. Bayan mutum ya yi gumin fuska idan wannan gumin ya bushe sai a ga wani abu kamar gishiri a kan hanci. Idan ba a dauki mataki da wuri ba hakan ke janyo kurajen hanci wadanda idan har sun fito sukan jima kafin su tafi. Akwai wadanda ke daukar shekaru kafin su tafi. Don haka a yau na kawo muku hanyoyi mafi sauki da za a bi domin magance wadannan ababen. Ga hanyoyin da suka kamata a bi don magance matsalar:

• A rage shiga rana idan rana ta yi zafi. Idan an shiga rana yakam janyo zufa hakan kuma na haifar da wadannan kurajen. Don haka ana amfani da man ‘sunscreen’ awa daya kafin a shiga rana.
• Za a iya tafasa ruwa sannan a rufe fuska da tawul a bokitin ruwan zafin domin turara fuskar a kullum kafin a shiga wanka. Yin hakan na fitar da maikon fuskar da ke haifar da gishirin hanci tare da kurajen kan hanci.
• Koren ganyen shayi na magance wadannan matsalolin. A tafasa ruwa tare da ganyen shayi sannan a turara fuskar da shi ko kuma ana goga ruwan da auduga safe da yamma a kullum kafin a kwanta barci.
• Amfani da man zaitun da ruwan lemun tsami na warkar da wadannan cutukan; a matse ruwan lemun tsami a cikin zuma sannan ana shafawa a fuskar. Sannan a shafa bayan ya yi mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi.
• Za’a iya amfani da ruwan kwai da zuma; idan aka hadasu sai a shafa a fuska ya jima kamar na mintuna talatin kafin a wanke da ruwan dumi.
• Kada a manta. A duk lokacin da aka yi amfani da ruwan dumi, ana so a sake wanke fuskar da ruwan sanyi domin rufe ramukan da gumin da datti ke shiga.