Kafa tana daya daga cikin gabban da suka kamata mu kula da su. Domin idan ba a kula da kafa ba, hakan na iya janyo kauje ko faso.
A rage dadewa a cikin ruwa idan an zo wanka. Yana da kyau a rika wanke tafin kafa da ruwan dumi ba tafasasshe ba.
- Muhimman batutuwan da za su mamaye taron Shugabannin Afirka a Habasha
- ’Yan Mali na murnar fatattakar jakadan Faransa daga kasarsu
Sannan yana da kyau ana shafa mai a kafa a duk lokacin da tafin kafar ya gamu da ruwa. Sa’annan a rage sanya takalma wadanda iska ba zai samu kafar ba.
- A tsoma tafin kafa a ruwan lemun tsami na tsawon minti 10. Yin hakan na fitar da matattun fata daga tafin kafa. Sannan a samu dutsen goge kafa a dirza ta.
- Za a iya hada man tafin kafa idan aka hada man zaitun da ruwan lemun tsami sai a rika shafawa a inda ta tsage. Ana girgiza wannan hadin kafin a yi amfani da shi a kullum.
- A rika shafa man basilin a tafin kafa, sannan a sa safa a kullum kan a kwanta barci.
- Kashi uku bisa hudu na kofin man kwakwa da rabin na man kadanya na gyara tafin kafa. Idan aka samo su sai a hada su sannan a narkar da su a wuta. Bayan sun narke, sai a shafa a tafin kafa sannan a sanya safa kafin a kwanta.
- Kada a tsoma kafa a ruwa salam haka, ba tare da an yi wa ruwan wani hadi da abubuwan da na lissafa ba.
- A rika shafa mai kafin a kwanta barci, sannan a sa safar kafa.