✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kula da fata a lokacin sanyi(2)

Yanzu da sanyi ya shigo, hazo da hunturu da iska da ake yi na sanya fatarmu ta lalace. Sai a ga mutum ya fara kauje…

Yanzu da sanyi ya shigo, hazo da hunturu da iska da ake yi na sanya fatarmu ta lalace. Sai a ga mutum ya fara kauje da kurarraji a fata. Yana da matukar mahimmanci a kula da fata, musamman a wannan lokacin. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwa da dama wadanda za ku bi don kare fatarku.
• A kasance cikin shan ruwa sosai kamar kofi 8 a rana. Yin hakan na dada hasken fata.
• A rika shafa man jiki kamar su ‘moisturizers’, yin hakan na kare fata daga zama mai gautsi.
• Kada a rika kwanciya da kwalliya a fuska. Yin hakan na sanya kurarrajin fuska. A wanke fuska da sabulun wanka kullum kafin a kwanta bacci.
• Yana da kyau a rage zama a cikin rana. Domin hakan na sanya maikon fuska da kuma sanya kurarraji da kuma canza wa fatar launi.
• Shin ko kun san cewa barci na dada kyau? Kwanciya da wuri domin samun barci na awa takwas (8) na dada lafiyar fata.
Abubuwan da za a yi don samin fata mai sulbi a hunturu.
• A kwaba ayaba da danyen madara sannan a shafa a fuska. A jira na tsawon mintuna 20 kamin a wanke da ruwan dumi. Hakan na sanya fata sulbi.
• A shafa kwababbiyar gwanda a fuska da wuya. Sai a jira na tsawon mintuna 15 kafin a wanke.
• A tafasa kabeji sai ana wanke fuska da ruwan. Yin hakan na gyara fata sosai.