Shugaban kasar China Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ta wayar tarho.
Kamar yadda fadar gwamnatocin kasashen biyu suka tabbatar, wannan shi ne kira na farko da shugabannin biyu suka yi tun bayan kaddamarwa kasar da Rasha ta yi.
- Za mu bullo da tsarin mafi karancin albashi a tamaula —UEFA
- Gobara ta yi ta’adi a kasuwar ’Yan Katako a Zariya
“Na yi doguwar tattaunawa mai ma’ana ta wayar tarho tare da shugaba Xi Jinping,” in ji Zelensky a shafin Twitter.
“Na yi imanin cewa, wannan tattaunawa da aka yi, da kuma nada jakadan Ukraine a kasar China, za su ba da kwarin gwiwa wajen raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.”
Mai magana da yawun Zelensky Sergiy Nykyforov ya bayyana a shafin Facebook cewa shugabannin biyu sun dauki kusan sa’a guda suna tattaunawar ta wayar tarho.
Bayan tattaunawar, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya nada sabon jakada a birnin Beijing na kasar ta China.
Pavel Ryabikin, wanda a baya ya jagoranci ma’aikatar masana’antu a kasar ta Ukraine, an nada shi a matsayin sabon manzon Ukraine a kasar China, a cewar sanarwar fadar shugaban kasar.
Ukraine dai ba ta da jakada a China tun watan Fabrairun shekarar 2021.
Gidan talabijin na CCTV na kasar China, ya ba da rahoton cewa, yayin tattaunawa a tsakanin shugabannin biyu, Xi ya shaida wa Zelensky, cewa tattaunawa ita ce kadai mafita a rikicin da ke wakana tsakanin kasarsa da Rasha.
Tashar talabijin ta CCTV ta bayar da rahoton Xi Jinping na cewa, kasar China na tsayawa tsayin daka kan batun zaman lafiya, kuma babban matsayinta shi ne inganta shawarwarin zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu.
Kasar China ta kuma sanar da cewa, za ta aike da tawaga zuwa kasar Ukraine da nufin neman hanyar warware rikicin siyasa a kasar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen, China, ta bayyana a wani taron manema labarai cewa, za a aike da wakilin gwamnatin kasar mai kula da harkokin yankin Eurasia, da zai ziyarci kasar Ukraine da sauran kasashen duniya, domin tattaunawa mai zurfi kan yadda za a warware rikicin kasar ta Ukraine, amma a siyasance.