Sabuwar dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta yi ta tanadiy hukuncin dandakewa da kuma kashe masu fyade a Jihar.
A ranar Laraba Majalisar ta amince da kwaskwarimar da ta yi wa Dokar Penal Code, bisa bukatar Gwamna Nasir El-Rufai, na tsananta hukuncin fyade wanda a baya daurin rai-da-rai ne a Jihar.
Shugaban Kwamitin Sadarwa na Majalisar, Tanimu Musa Kachia ya bayana wa Aminiya cewa sabbin tanade-tanaden dokar.
“Dun wanda aka kama da laifin yi wa yaro dan kasa a shekara 14 fyade to za a dandake shi a kuma kashe shi.
“Duk wanda ya yi jima’i da yaro dan kasa da shekara 14 to za a yanke masa hukuncin dandakewa da kuma kisa.
“Idan aka kama mace da laifin yi wa yaro fyade to kotu za ta yanke mata hukuncin bilateral salpingectomy sannan a kashe ta.
“Idan wanda aka yi wa fyaden ya haura shekara 14, to za a yi wa mai fyaden dandaka da daurin rai-da-rai.
“Idan wanda ya yi fyaden karamin yaro ne, to kotu za ta ba da umarnin a sanya sunasa a rajistar masu manyan laifuka sannan Antoni Janar ya wallafa a kafafen yada labarai.
“Idan shari’ar fyaden ta shafi yara ‘yan kasa da shekara 14 ne, to wajibi ne a bukaci rahoton asibiti”, inji shi.