✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za a bunkasa noman Masara a Najeriya — Masana

A shekaru biyar na gwamnatin Buhari, Najeriya tana noma masara tan miliyan 10.8 duk shekara.

Kamfani Bayer Nigeria Limited, ya shirya wani gagarumin taron da ya hada na masana da sauran masu ruwa da tsaki kan noman masara a Najeriya don tattaunawa kan kalubale da hanyoyin bunkasa noman masara a Najeriya.

Taron ya yi bayanin kan babban kalubalen da ke gaban manoman masara a Najeriya, na bukatar masara da masu gidajen kaji ke yi.

Har’ila yau taron ya yi bayanin hanyoyin da manoman masarar za su bi su magance wannan babban kalubale da ke gabansu, ta hanyar bunkasa noman masarar da suke nomawa a Najeriya.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar manoman masara ta Najeriya, Dokta Bello Abubakar Funtua, ya bayyana cewa yanzu Najeriya tana samar da masara ninki goma na masarar da take samarwa kafin Najeriya ta sami ’yancin kai.

Ya ce daga shekarar 1999 zuwa shekara ta 2019, a duk shekara masarar da ake nomawa a Najeriya tana ninkawa sau biyu.

‘’Wannan ya sanya daga shekara ta 2014 zuwa shekara ta 2019 Najeriya ta zama kasa ta biyu kan noman masara a Afrika a inda take noma masara tan miliyan 10.8 a duk shekara baya ga Afrika ta Kudu wadda take kan gaba a noman masara a nahiyar Afrika, da take noma masara tan miliyan 12.9 a duk shekara.

Dokta Bello, ya yi bayani cewa shekara ta 2014 Najeriya ta noma masara tan miliyan 10.1 inda a shekara ta 2015 kuma ta noma tan miliyan 11.6, sai a shekara ta 2016 da ta noma tan miliyan 11.6, sai shekarar 2017 ta noma tan miliyan 10.4, a shekara ta 2018 zuwa shekara ta 2019 ta noma kimanin tan miliyan 11.0.

Dokta Bello ya ce, a shekaru biyar na gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Najeriya tana noma masara tan miliyan 10.8 a duk shekara.

Ya bayyana cewa, masarar da Najeriya ta noma a shekara ta 2019 tan miliyan 12.6 ta yi kasa idan aka yi la’akari da wadda ta noma a shekarar 2020 a sakamakon matsalar karancin ruwan sama, inda aka noma masara tan miliyan 12.4 sakamakon matsalolin ambaliyar ruwa da karancin taki a wasu sassa na yankankunan kudu maso-gabas da kuma Arewa ta gabas da Arewa ta yamma.

A nasa jawabin Darakta Janar na Majalisar samar da iri ta Kasa [NASC], Dokta Philip Ojo, ya bayyana mahimmancin irin shuka na masara kan bunkasa harkokin noman masara.

Ya ce, ya zuwa yanzu an samar da irin shuka na masara daban-daban har 140, don ganin an bunkasa noman masara a Najeriya.

Wani babban jami’i a Kamfanin na Bayer wadan da suka dauki nauyin shirya wannan taro, Mista Joseph Kibaki ya bayyana cewa, wannan Kamfanin yana iyakar kokarinsa wajen ganin ya bunkasa harkokin noman masara ta hanyar kawo tsare-tsaren hanyoyin zamani a fannin noman masara.

Masanan da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun amince cewa noman masara ya yi kasa a Najeriya amma sun kawo shawarwari kan hanyar da za a bi wurin bunkasa noman masara a Najeriya ta hanyar yin amfani da ingantaccen irin shuka da kayayyakin noma na zamani.