Gwamnatin Tarayya ta sanar da yadda za a dawo da harkokin jirgin sama, farawa da Abuja da Legas daga ranar 8 ga watan Yuli 2020.
Da yake sanar da haka a ranar Laraba, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya ce tashoshin jiragen da ke Kano da Fatakwal da Owerri da Maiduguri, za su koma aiki daga ranar 11 ga watan na Yuli.
Sanarwar dawowar jigilar jiragen sama a cikin gida ta ce, “Za a bude sauran tashoshin jirgin sama ranar 15 ga wata. Nan gaba za a sanar da na [jigilar] kasa da kasa”.
Da farko gwamnatin ta sanar da karin sassauci a kan dokar kullen COVID-19 da ya hada da bude tafiye-tafiye tsakanin jihohi da shirin bude makarantu ga dalibai masu jarabawar kammala karatun firamare da sakandare.
Mutum fiye da 10,000 sun warke daga COVID-19
Zuwa yanzu wandanda suka warke daga COVID-19 sun haura 10,000 a Najeriya, daga cikin mutum 26,488 da suka kamu. Ta kashe mutum 603 daga cikin adadin, wasu 15,729 kuma an killace su.
A ranar 1 ga watan Yuli da Hadi Sirika ya yi sanarwar, alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna mutum 790 ne suka kamu da cutar a ranar.
Matakan kariya a filayen jirgin sama
Gagbanin nan kwamitin shguaban kasa na yaki da cutar ta coronavirus da NCDC sun bayyana matakan kare yaduwar cutar da aka a dauka filayen jirgin da ke Abuja da Legas kafin a sake bude su, wata uku bayan rufe sufurin jiragen sama a Najeriya sakamakon bullar cutar.
Matakan kariyar da Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dauka a tashoshin sun hada da:
- Manyan injina da za su rika tantance fasinjoji.
- Zanen alama a wuraren da matafiya ke bin layi da tazara a tsakaninsu.
- Bayar da tazara tsakanin kujerun zama a harabar tashoshin.
- Tazara a tskanin kujerun fasinjoji a cikin jirage.
- Kayan kariyar COVID-19 a tashoshin.
- Sunadaran wanke hannu.
- Na’urorin auna dumin jiki.
- Zanen alamar bayar da tazara domin tunatarwa.
In ba a manta ba NCAA ta sanar da shirin bude tashoshin jirgin sama domin ci gaba da harkokinsu bayan an rufe su da nufin kare yaduwar cutar coronavirus.