Tsohon dan wasan Ajax kuma dan asalin kasar Dimokuradiyya Kongo, Jody Lukoki, ya rasu sakamakon bugun zuciya da ya kamu da shi bayan dukan kawo wuka da ’yan uwansa suka yi mishi.
Rahotanni daga kasar Netherlands sun nuna Lukoki ya kamu da ciwon ne bayan musu ya barke tsakaninsa da ’yan uwansa, har ta kai ga bai wa hamata iska a tsakaninsu.
- Dole su Amaechi da Ngige su ajiye aiki cikin kwana 5 —Buhari
- Wahalar man fetur da ake fuskanta a yanzu somin tabi ce —Dillalan Mai
Tuni jami’an tsaro suka kaddamar da bincike don gano hakikan abin da ya faru.
Jody Lukok, dan asalin kasar Dimokuradiyya Kongo, ya fara taka leda ne da kungiyar kwallon kafa ta Ajax, ya rasu yana da shekara 29 a duniya.
Kafin rasuwarsa, Lukoki ya sauya sheka zuwa FC Twente da ke kasar Faransa, amma bai buga mata wasa ba sakamakon mummunan raunu da ya samu a guiwarsa a wurin atisaye.
Ya kuma murza leda a kungiyoyin kwallon kafa irin su SC Cambuur da PEC Zwolle da Ludogorets Razgrad II da Ludogorets Razgrad da kuma Yeni Malatyaspor.