✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan Najeriya suka fifita zuwa yakin Ukraine sama da zama a kasarsu

“Na rantse da Allah in da ina da kudin da zan biya na tafi.”

Yayin da gwamnatin Najeriya ke jigilar kwaso ’yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a Ukraine bayan ruwan bama-bamai da kasar Rasha ke ci gaba da yi a babban birnin kasar, Kyiv, wasu ’yan Najeriyar da ke zaune a gida su kuma sun bayyana aniyyar zuwa a fafata da su domin taimakawa kasar ta Ukraine.

Bayan mutum sama da miliyan daya sun tsere daga kasar Ukraine wadda Rasha ta far wa da yaki, matasan Najeriya na rububin sauya sheka zuwa can domin yin fito-na-fito da sojojin Rasha, wadanda a mako guda suka mayar da wasu sassan kasar tamkar kufai tare da kwace tashoshin nukiliya.

Da dama daga cikin wadanda suka nuna goyon bayan sun yi gangami a kofar Ofishin Jakadancin Ukraine da ke Najeriya domin a sahale musu zuwa kasar domin su tayar kasar gwabza yakin da take yi da Rashar.

Tuni dai ’yan kasar da dama suka dauki damara suka fita a fafata da su domin kare martabar kasarsu amma kuma wasu sun nemi hanyar tserewa zuwa wasu makwabtan kasashen da ke zaune lafiya kamar Poland, domin tsira da rayuwarsu.

Wannan ya sa jami’an kula da iyakokin kasar Ukraine din tilasta wa matasan kasar maza da su koma domin a fafata da su a wannan yaki.

A cikin wannan hali ne kuma wasu ’yan Najeriyar ke fifita zuwa ko za a kashesu a can fiye da su ci gaba da zama a Najeriyar.

Sai dai kuma duk da halin da kasar Ukraine din take ciki na bukatar mutanen da za su taimaka mata a wannan yakin kamar yadda ya bayyana karara cewa dakarun Rasha sun ninka na Ukraine din nesa ba kusa ba, kasar Ukraine din ta gindaya wasu sharudda da dole sai mutum ya cika domin samun damar zuwa a fafata da shi.

Daga cikin sharuddan da Ukraine din ta gindaya ciki har da biyan dalar Amurka dubu daya da kuma shaidar samun horo a sha’anin tsaro a kasar da mutum yake.

Kazalika, a wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta ce ba za ta kyale ‘yan Najeriyar shiga cikin mayakan da ke yaki da Rasha a kasar Ukraine ba kuma wannan yunkuri abin takaici ne.
Bugu da kari ofishin jakadanci Ukraine da ke Najeriya ya nesanta kansa daga rahotannin da ke cewa ya bukaci dukkan dan Najeriyar da ke son shiga yakin da ya biya dalar Amurka 1,000 a matsayin kudin tikitin jirgin sama da na biza kamar yadda sashin Hausa na BBC ya rawaito.

Dangane da dalilin da ya sa wadannan nan mutane ke zumudin zuwa domin a gwabza wannan yakin da su, Aminiya ta binciko tare da zantawa da wasu daga cikin wadannan mutane domin samun tabbacin dalilansu na son zuwa wannan yaki duk da cewa sun sani sarai za a iya kashesu a filin daga.

Wasu na ganin irin rayuwar da ake ciki a Najeriya ta talauci da hauhawar kayan masarufi da rashin aikin yi ga wadansu mutane shi ne babban dalilin da ya sa wasu suka fifita zuwa yakin sama da ci gaba da zamansu a Najeriya cikin halin da suke ciki.

Amma sai dai wasu ka iya tambayar wadannan masu wannan ra’ayi kan me ya sa tun da ake samun rikice-rikice a Najeriya ba su taba zuwa sun taimaki sojojin Najeriyar domin a kawo karshen matsalar ba, rashin kishin kasa ne ko kuma me za a ce?

A zantawar da Aminiya ta yi da wani matashi wanda ya ciza ya yatsa sakamakon rashin kudin da zai biya domin tafiya zuwa a fafata wannan yaki da shi, Ibrahim Abdulyakin, mazaunin Abuja, ya shaida wa Aminiya cewa, matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya ba wai yaki bane tsakanin Najeriya da wata kasar yaki ne na cikin gida tsakanin ‘yan Najeriya, kuma wannan salon yakin sam ya sha bambam da wanda ke faruwa a Ukraine.

A Ukraine a fahimtarsa dakarun sojojin Rashar ba kashe fararen hula a Ukraine din suke yi ba.

“Na rantse da Allah in da ina da kudin da zan biya na tafi, da in zauna a nan na mutu da yunwa ba gwamma na tafi can na je in na yi sa’a shikenan na zama dan can ba.

“Na san mawuyaci ne na mutu a can saboda sojojin Rasha ba mutane suke kashe wa ba bukatarsu kawai su kwace ikon kasar, sai dai idan ta zo da karar kwana kuma dama ko ina nan zan iya mutuwa, ‘yan bindiga da boko haram da ma sun hana mu sakat.

A bangare guda kuma, Usman Zilkifl Ibrahim, wanda  matshi ne wanda ya kammala bautar kasa kuma yake kan neman aikin da zai yi domin rufawa kansa asiri ya ce “duk matashin da zai budi baki ya ce zai je a fafata da shi a wannan yaki to ta tabbata wannan matashi bai san me ke damunsa ba kuma ba shi da hangen nesa a rayuwa”

“Shekara nawa a na fama da yakin Boko Haram a Najeriya sun taba tunanin zuwa su taimaka, to kana jin wannan ka san rashin tunani ne da dakikanci ga matashi mai karfi a jiki ya ce zai tafi kasar Ukraine domin taimaka musu a yaki da suke ciki”

“Mutum mai tunani mai kyau wanda ya ke da kudiri na ganin ya kawo sauyi ga kansa da ma kasa baki daya ba zai yi wannnan mummunan tunani ba.”