✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘yan Najeriya ke martani kan cin zarafin da Sanata Abbo ya yi wa wata mata  

Daya daga cikin batutuwan da suka haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta na zamani, cikin sa’o’i 48 da suka wuce, shi ne fitar…

Daya daga cikin batutuwan da suka haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta na zamani, cikin sa’o’i 48 da suka wuce, shi ne fitar da faifan bidiyon nan da ya nuna Sanata Elisha Ishaku Abbo, mai wakiltar Arewacin jihar Adamawa, a majalisar dattawan Najeriya, inda a ciki ya ke muzanta wata mata mai shayarwa.

Bidiyon ya nuna Sanatan yana cin zarafin matar bayan ta saka baki cewar ya daina muzgunawa ‘yar zaman kantin sayar da robobin jima’In—wanda Sanatan ya ce ta kyarace shi. Kwatsam sai dan majalisar ya koma kan wannan matar, inda ya sauke fushinsa a kanta, ta hanyar duka tare da marin ta a kunci.

Wannan danyen aikin da Sanatan ya aikata, ya jawo muhawara daga bangarorin Najeriya daban daban, inda wasu ke kiran da lallai sai an gurfanar da Sanatan gaban shari’ah, dan ya fuskanci hukuncin cin zarafi.