✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan Najeriya ke kokawa bayan litar fetur ta kai N600

An ninka kudin sufuri a yayin da ’yan bumburutu da gidajen mai suke cin karensu babu babbaka.

Masu ababen hawa da fasinjoji na guna-guni bayan karancin man fetur ya sa ana sayar da lita a kan N600 a yayin da ’yan bumburutu da gidajen mai suke cin karensu babu babbaka.

’Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan karancin man da ya sa a wasu wuraren aka ninka farashin sufuri, a yayin da ake zargin wasu gidajen man da tsawalla farashi.

Karancin man ya sanya masu neman ababen hawa na haya yin cirko-cirko a kan tituna Abuja da Kano da Fatakwal, inda gidajen mai ke sayar da lita a kan N190 zuwa N400, mai makon N165 da gwamnati ta kayyade.

Wasu gidajen mai kuma suna a rufe, ba su da man, ga kuma dogayen layukan ababen hawa a gidan da ke da shi, wadanda su kuam ake korafin sun tsawwala farashin.

Tun a makon jiya ne dai matsalar karancin mai ta kankama a Najeriya, bayan dan kwangialar Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya shigo da gurbataccen mai lita miliyan 100.

Ba a kai ga gano hakan ba, sai da wasu gidajen mai suka fara sayarwa, har ya fara lalata ababen hawa.

Tuni dai  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu a matsalar da aka samu.

Tun a makon jiyan da aka fara samun karancin mai Shugaban NNPC, Mele Kyari, ya bayar da tabbacain shawo kan matsalar cikin gaggawa, amma har yanzu bata kau ba.

Cunkoson ababen hawa a wani gidan mai a Kano. (Hoto: Lubabatu I. Garba).

Karancin zai haddasa hauhawar farashi —NBS

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce karancin man na iya ta’azzara matsalar hauhawar farashin kayayyaki na wani lokaci, wanda kuma ke iya girgiza tattalin arziki, idan ba da dauki matakin dakilewa ba

“Ko an ki, ko an so, masu sufuri za su yi amfani da damar su kara kudin jigilar kaya.

“Shi kuma dan kasuwa dole idan ya tsahi sayar da kayansa ya kara wani abu saboda shi ma kudinsa ya fita.”

Dogayen layi

Ana ci gaba da samun dogayen layuka a gidajen mai a yayin da kamfanonin mai suka tabbatar cewa a halin yanzu ba a lodin mai yadda ya kamata a dafo-dafo.

An ninka farashin sufuri a Abuja

Mutanen da ke jiran ababen hawa a Abuja sun bayyana damuwa game da halin da suka tsinci kansu a ciki.

Sun kuma yi kira ga NNPC da sauran masu-fada-da-a-ji da su yi wa al’ummar Najeriya bayanin hakikanin abin da ke faruwa.

Su kuma ’yan bumburutu masu sayar da man fetur a jarka, suna sayar da lita daya a kan N500 zuwa N600 a Abuja, ya danganci wuri da kuma yadda mai saya ya daidaita da su.

Aminiya ta lura yawancin gidajen mai a yankunan Kubwa, Berger, Wuse da sauran yankunan da ke wajen garin Abuja ba su da mai.

Daga Kubwa a Abuja zuwa Zuba a Jihar Neja da kuma Mararaba a Jihar Nasarawa, daruruwan masu hawa motocin haya ne suka yi cirko-cirko a kan titi suna jira abin hawa, a yayin da wasu suke takawa a kasa.

Wani fasinja ya ce, “Mun dauka karancin mai ya zama tarihi a kasar nan, amma ga shi ya dawo. Jiya N500 na biya daga Area 1 zuwa Kubwa, wanda bai wuci N250.”

Kazalika kamfanonin sufuri na Bolt da UBER su ma sun kara farashinsu na sufuri.

Karancin ababen hawa a Kano

Matsalar karancin man a Kano ta kawo karancin zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna a yayin da mutane fargabar cewa mastalar na iya haifar da tashin farashin kayan masarufi.

Gidajen mai da dama sun kasance a rufe, ’yan kalilan din da ke sayarwa kuma a shake suke da dogayen layuka masu saye.

Masu shan man da muka zanta da su sun shaida mana cewa gidajen mai na cin karensu babu babbaka, suna sanya farashi yadda yaga dama, sabanin farashin da gwamanti ta kayyade na N162 zuwa N165 a kan kowace lita.

Wasu gidajen man da muka zagaya suna sayar da lita a kan N190 zuwa N200.

Harkoki sun tsaya a Legas

Karancin man ya tsayar da harkoki da dama a Legas, inda babban titin LASU zuwa Egbeda ke fama da cunkoso saboda dogayen layin ababen hawa a gidajen mai.

Gidajen man NNPC a Legas na sayar da fetur a kan farashin gwamnati, sauran gidajen mai kuma na sayarwa daga N180 zuwa N200. A wasu wuraren kuma farashin ya kai har N250 kowace lita.

Aminiya ta gano yada karancin man ya janyo kasuwar ’yan bunburutu ta bude inda suke sayar da man a kan farashin da suka ga dama.

A yankin Alaba Rago da ke Ojo, wani dan bumburutu, Abdullahi Adamu, ya ce yana sayar da lita a kan N250.

“Gidajen mai suna sayarwa da dare. Wani lokaci da tsakar dare suke sayar wa irinmu. Muna yin kari ne saboda wahalar da muke sha a cikin dare,” inji shi.

Idris Ado, wani dan bumburutu da muka zanta da shi a Kano, ya bayyana cewa duk da cewa suna samun kudi sosai saboda karancin man, amma ba su goyon bayan a ci gaba da samun karancin man a fadin kasar nan.

“Gaskiya ne muna samun kudi sosai a wanann lokaci amma muna fatan a kawo karshen wannan matsala. Idan kin duba yawancin al’umma suna cikin matsala.”

Za mu kawo lita biliyan 2.3 a mako biyu — NNPC

A yayin da matsalar ke ci gaba, NNPC ya ba da izinin dako da kuma sayar da ma na sa’a 24 a kowane mataki.

NNPC ya ce tuni manyan kamfanoni da gidajen mai suka fara aikin dako da kuma sayar da mai na tsawon awa 24 domin tabbatar da ya watada a kasar.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce NNPC yana shirin adana lita biliyan 2.3 na man fetur a cikin mako biyu masu zuwa.

Hakan, a cewarta zai tabbatar da samuwar wadataccen mai na tsawon wata guda a fadin Najeriya ba tare da wata tangarda ba.

Don haka ya shawarci jama’a da kada su tayar da hankalinsu su rika sayen mai tare da fargabar cewa za a samu karancinsa a nan gaba.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Simon E. Sunday, Faruk Shuaibu, Seun Adeuyi (Abuja), Abubakar Akote (Minna), Salim U. Ibrahim, Sadiq Adamu (Kano), Victor Edozie (Port Harcourt) & Eugene Agha (Legas)