✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka yi garkuwa da masu hakar ma’adinai 100 a Zamfara

Sun bindige 10 daga ciki suka mamaye wurin hakar ma'adinai, inji Sarkin Anka

Masu hakar ma’adinai kimanin 100 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a rana guda a yankin Kananan Hukumomin Maru da Anka a Jihar Zamfara.

Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, ya ce ’yan bindigar sun kuma kashe mutum 10 tare da mamaye wani wurin hakar ma’adanai a yankin.

Sarkin Anka ya sanar da haka ne yayin tattaunawa da Mayan Hafsoshin Tsaro a Gusau, lokacin da suka ziyarci Jihar ranar Talata, inda suka gana da Gwamna Matawalle da kwamandojin soji kan kawo karshen mastalar ’yan bindiga da ke ci wa jihar tuwo a kwarya.

Basaraken wanda ya ce ’yan bindiga ba sa ga-maciji da masu hakar ma’adinai a jihar, ya ce labarin garkuwa da aka yi da masu hakar ma’adinan a ranar 2 ga Maris bai bazu sosai ba saboda a lokacin hankula sun karkata ne kan batun sace Dalinayn Makarantar Jangebe.

“’Yan bindiga sun addabi masu aikin hakar ma’adanai tare da kwace musu kudade da dukiyoyi.

“Akwai rashin jituwa tsakanin masu hakar ma’adanai da ’yan bindiga a jihar.”

Ba amfanin hana tashin jirgi a Zamfara

Sarkin ya yi mamakin dokar hana tashin jirgi da Gwamnatin Tarayya ta sanya a Jihar bisa zargin hadin bakin ’yan bindiga da masu hakar ma’adinai wajen fasakwaurin makamai da kuma musyarsu da zinaren da aka hako.

“Mun yi mamakin sanarwar ‘hana shawagin jirgi’ da aka sa wa jiharmu kan zargin fasakwaurin makamai da kuma hakar ma’adanai ba bisa ka’ida, alhali ko filin jirgi jihar ba ta da shi.

“Akwai jihohin da fi Zamfara fama da matsalar tsaro, muna sa ran idan za a bayar da irin wannan umarnin su ma ya hada da su.

“Mutanenmu masu aikin hannu da ke de kananan lasisin hakar ma’adinai sun taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin jihar, sun kuma taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar ’yan gudun hijira a jihar ta hanyar tallafa musu,” inji shi.

Bukatar kara jami’an tsaro

Ya kuma yi kira da a kara yawan jami’an tsaro don yakar ’yan ta’adda a jihar.

“Shirin samar da zaman lafiya da tattaunawar da gwamnanmu ya yi ya zama dole saboda a yanzu muna jami’an tsaro da muke da su 5,000 ne da ke yaki da ’yan bindiga l 30,000.”

Sarki Attahiru ya tabbatar wa manyan shugabannin tsaron cewa mutanen jihar za su ci gaba da yi musu addu’ar samun nasara.

Ya kuma bukaci Babban Hassan Tsaro, Lucky Irabor da ya tabbatar da hadin kai tsakanin dukkannin bangarorin sojin yayin gudanar da ayyukansu don toshe duk wata kafa ga masu aikata laifi.

Da yake amsawa, Shugaban Hafsoshin Tsaron ta yaba da rawar da sarakunan suka taka wajen yaki da aikata laifuka sannan ta bukace su da su ci gaba da jan hankalin mabiyansu wajen ba da sahihan bayanai da za su kai ga kame ’yan ta’adda.

A nasa jawabin, Gwamna  Matawalle ya ba da tabbacin gwamnatinsa na karfafa zaman lafiya da tattaunawa tare da tallafa wa hukumomin tsaro wajen ci gaba da kai hare-hare kan ’yan bindiga da ba su tuba ba.