✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa kauyukamu suka hana mu zuwa gona’

Al’ummar Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna sun bayyana yadda suka watse suka bar gidajensu da gonakinsu sakamakon hari da wadansu ’yan bindiga suka…

Al’ummar Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna sun bayyana yadda suka watse suka bar gidajensu da gonakinsu sakamakon hari da wadansu ’yan bindiga suka kai musu a ranar Lahadin  da ta gabata.

Aminiya ta samu bayanin cewa lamarin ya faru ne bayan wadansu ’yan sintiri sun shiga daji da nufin tunkarar ’yan bindigar da suka dade suna matsa wa al’ummar yankin.

Wakilinmu wanda ya ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar, inda ya ruwaito cewa mata da yara kanana kusan 1200 ne ke suka nemi mafaka a makarantar firamare ta Birnin Yero a Karamar Hukumar Igabi da ke jihar. Akwai kuma bayanan da ke nuna cewa kusan kauyukan da abin ya faru manoma ne da ke kan iyakar Birnin Gwari da garin Kaduna.

Bayanai sun nuna cewa ’yan bindigar ba su kashe kowa a kauyukan ba a ranar Lahadin sai dai kawai suka umurce su da su bar garuruwan.

Mai unguwar Gide, Jibril Abdullahi daya daga cikin masu gudun hijirar  ya bayyana sunayen kauyukan da aka tarwatsa da cewa akwai Jura da Unguwar Gide da Unguwar Dan Gauta da Unguwar Nayawo da Unguwar Makeri da Kigani da Sabon Gida da Dallatu da Unguwar Ahmadu da Sabon Gari.

Sauran sun hada da Kusau da Gidan Sarkin Noma da Unguwar Pati da Unguwar Amfani da Unguwar Tofa da Soron Giwa.

Ya kuma bayyana cewa akasarinsu manoma ne amma sai da ya kwashe kusan kwana 25 bai shiga gonarsa ba saboda tsoron barayin.

“Duk da na zuba kusan Naira miliyan biyu a gonar, amma na kasa shiga domin yin zagaya saboda gudun me zai biyo baya. A yanzu haka maganar da muke yi da kai sai da na kwashe kwana sama da 25 ban shiga gonar ba.

“Yanzu haka mata na uku da ’ya’ya amma ban ga matata daya ba da ’ya’yana kuma ga shi duk mun baro garin bayan ’yan ta’addan sun nemi mu watse saboda kawai ’yan sintiri sun bi su cikin daji da nufin tunkararsu kasantuwar suna yawan damunmu a wannan yanki,” inji shi.

Shi ma Salisu Lawal wanda ya tabbatar da mutuwar uku daga cikin ’yan sintirin da suka shiga daji neman barayin ya bayyana sunayensu cewa akwai Danbirni da Yushehu da kuma Tukur wanda yaro ne ga mai Unguwar Bakin Kasuwa.

Ya kuma kara da cewa a yanzu haka akwai sauran ’yan sintirin wadanda ya ce ba su gani ba tun bayan shigarsu cikin dajin.

“Mu a yanzu burinmu shi ne mu koma gida abin da kawai muke bukatar gwamnatin jihar ta yi mana ke nan domin mu muna da iyali kuma muna da abin yi saboda haka ba dadi muke ji muzauna a nan ba, “ inji shi.

Idris Saidu wakilin Sarkin Jura ya shi a gida ya kwana amma ya taso ne domin ya ziyarci al’ummar su dake gudun hijira a makarantar firemare dake Birnin Yero.

“Wannan gwamnati an ce mai adalci ce idan kuwa ita mai adalci ce ga aikin adalci ya zo. Muna kuma son a yi mana adalci domin mu dai a yanzu halin da muke ciki a yankinmu akwai mai ciyar da mutum talatin amma yanzu ya zo nan sai an ba shi abinci ya ci. Ka ga harka ta lalace.

“Domin wannan gwamnati ta ce mu yi noma mun yi noman an kuma ce da mu ba za mu dauki mu kawo gida ba. Saboda ’yan ta’adda sun hana mu zuwa gona. Idan mun je da yara sai a zo a kwashe mana su. Halin da muke ciki ke nan a yanzu,” inji shi.

Kkakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo cewa yayi mazauna kauyukan da ke kusa da wajen ne da suka samu labarin abin da ke faruwa a yankin na su sai suka baro can saboda tsoro.

Ya kuma bayyana cewa ba a kai hari kauyukan ba sai dai kawai al’ummar sun baro can ne zuwa firamaren saboda tsoro. Ya kuma bayyana cewa ’yan sanda sun shiga cikin batun kuma har wasu mazauna garuruwan sun fara komawa garuruwansu.