✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka halaka ’yan sanda 5 a Jihar Ribas

A Juma’ar makon jiya ce, wasu da ba a san ko su waye ne ba, amma ake kyautata zaton mahara ne suka yi wa wasu…

A Juma’ar makon jiya ce, wasu da ba a san ko su waye ne ba, amma ake kyautata zaton mahara ne suka yi wa wasu jami’an ’yan sanda 5 a Jihar Ribas kwanton bauna, suka yi masu kisan gilla.
Al’amarin ya faru ne a yankin Okogbie da ke karamar Hukumar Ahoada, yankin da ke fama da yawan tashe-tashen hakali da ta’addanci da ake danganta shi da matasa ’yan kungiyar asiri.
Lamarin ya rutsa da jami’an ne da ke aiki da runduna ta 30 ta ’yan sanda na PMF da ke Bayelsa, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa can ne bayan sun dawo daga wani aiki na musamman da sukaje yi Jihar Yobe.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ribas, Musa Kimo ya yi Allah wadai da aikin ’yan ta’addan kuma ya sha alwashin rundunar sa sai ta zakulo makasan.
Rundunar ta sanar da sunan jagoran ’yan sandan da DSP Nasiru Halidu da kuma sauran wasu kurata hudu. Da yake yi wa manema labarai karin bayani ta hanyar jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ahmad Muhammad, Kwamishinan ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar duk wani mataki na ganin wadanda suka yi wannan ta’annati sun fada komarsu. “Yau rana ce ta matukar bakin ciki ga wannna runduna na kashe mata zarata biyar, musamman irin yadda ba su gajiyawa wajen tunkarar duk wani kalubale na tsaro da aka tura su.” Inji shi.
Ya kara da cewa motaci biyu da jami’an ’yan sandan ke tafiya da su, a yayin harin daya ta tsallake, sai wannan ta bayan kaddarar ta fada mata.
Aminiya ta zanta da wani dan uwan jagoran tafiyar mai suna Komred Isa Halidu Maishanu a gidan iyayensu da ke garin Suleja ta Jihar Neja, jim kadan bayan jana’izar dan uwan nasa marigayi DSP Nasiru Halidu Maishanu, a ranar Talata da ta gabata, inda ya yi bayani kamar haka:
“Shi dai dan uwana Nasiru ya bar garin Damaturu a ranar Juma’a da ta gabata tare da abokan aikinsa su biyar a cikin motarsa kiran jif kuma shi ke jan motar, a yayin da wasu na kasa da shi kuma wanda ban san hakikanin adadinsu ba ke cikin motar ’yan sanda, kamar yadda ya sanar da ni bayan sun fara tafiyar. Hakan ya biyo bayan kammala aiki na musamman ne da a ka tura su yi a Jihar Yobe wanda suka shafe watanni a wajen. Shi ne jagorar tafiyar, na yi ta zantawa da shi ta waya a yayin tafiyar ta su har zuwa wani lokaci a ranar. Ita motar wajen aikin nasu ta yi ta baci a kan hanya suna shawo kanta amma dai ya dage a kan sai dai su ci gaba da tafiya tare tun da shi ne jagoransu ba zai tafi ya bar su ba.
“Daga baya da ya ga tafiyar tasu ba za ta tafi daya ba, sai ya yanke shawarar daya motar ta yi gaba, bayan jimawa shi sai ya ta so. To ana cikin irin haka din ne sai ya ci karo da wadanda suka yi ajalinsu da misalin karfe goma sha biyun daren Juma’ar, kamar yadda labari ya zo mana. A lokacin ita motar ’yan sanda tana gaba.
“Wadanda suka kashe su din sun tsare hanya ne kamar masu binciken hanya, shi da ke jan motar sai ya fito ya bayyana kansa gare su, suka sara masa. Ya juya zai shiga mota ke nan sai su ka bude masa wuta suka kuma bude wa wadanda ke cikin motar wuta. Kashegari ne bayan labari ya kai ga hukuma, daya ayarin suka dawo aka kwashi gawarwakinsu tare da motar. Wannan shi ne bayani da muka samu daga wajen wani namu da ke yankin, wanda ya bi diddigin al’amarin bayan labari ya zo mana a ranar Asabar, kuma irin bayanin ke nan da ’yan sanda da suka kawo gawarsa a ranar Talata tare da ta wasu mamatan, suka tabbatar mana.” Inji Isa Halidu.
dan uwan marigayin ya ce, marigayi Nasiru Halidu Maishanu wanda bai ida cika shekara arba’in ba da haihuwa, ya halarci Jami’ar Bayero da ke Kano bayan ya gama wata makarantar ’yan sanda da ke Jos. Ya riki mukamin mataimakin shugaban babban ofishin ’yan sanda wato DCO a garin Zuba na yankin Abuja, kafin ya wuce makarantar ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke Gwoza a Jihar Borno, inda ya yi kwas a bangaren na watanni.
Bayan nan ne, inji shi, aka yi masa sauyin wurin aiki zuwa Jihar Bayelsa, kuma daga can ne aka tura su aiki na musamman a Jihar Yobe wanda ya gama a kwanan nan.
Ya ce an ba su hutun mako biyu bayan kammala aikin, inda ya dawo gida Suleja amma bayan mako guda sai aka bukaci ya dawo kuma daga nan ne aka maida su wajen aikin nasu na ainihi; inda rai ya yi halinsa. Ya bukaci hukuma da ta gudanar da bincike a kan al’amarin mutuwar tasa, inda ya ce akwai ayar tambaya a kan al’amarin game da hakikanin wadanda ake zargin sun yi kisan; daga abokan adawa ne ko kuma al’amari ne na cikin gida da ya shafi wajen aiki? Sannan kuma an hada su da mota da ta rika lalacewa a hanya. Ya rasu ya bar mahaifansa biyu, da matar aure da kuma ’ya’ya biyu mace da namiji.