Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin tunawa da Ranar Ma’aikata ta bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan a madadin gwamnatin a wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar, Aishetu Gogo Ndayako, ta fitar ranar Talata a Abuja.
- Shari’ar Dakatar da Ganduje: Kotu ta tsayar da ranar 27 ga Mayu
- Sanatoci sun yi rikici kan sauyin kujeru a zauren Majalisa
Tunji-Ojo ya sake nanata buƙatar samar da ayyuka masu inganci da daidaito a dukkan ɓangarorin aiki, yana mai jaddada ƙudirin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa al’adu, ƙirƙire-ƙirƙire, samar da aiki da haɗa kai a wuraren aiki.
“A daidai lokacin da taken bana, wanda ya mayar da hankali kan tabbatar da tsaro da lafiya a wurin aiki a cikin sauyin yanayi, ina so in bayyana cewa, Gwamnatin ta yi tsayin daka kan ƙudurinta na ba da fifiko ga tsaro da jin daɗin dukkan ’yan ƙasa.
“Ins sake jaddada aniyar shugaban ƙasa na samar da yanayi mai kyau na aiki, inda kowanne ma’aikaci zai iya bunƙasa kuma ya ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban ƙasa”.
Yayin da yake amincewa da gudummawar da ma’aikata ke bayarwa, ya yi kira da a ɗauki ƙwararan matakai don daƙile illolin sauyin yanayi ta hanyar haɗa kai wajen aiwatar da ayyuka da tsare-tsare masu ɗorewa a wuraren aiki da kuma gina ƙasa bisa ƙa’idojin amincewa da himma wajen gudanarwa.
Ministan ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa kan tsarin ajandar gwamnati mai ci yayin da ya yi wa ma’aikata fatan alheri.