✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan Amotekun suka fara ‘wuce gona da iri’

Ana zargin su kisa, da ta hankalin jama'a da wuce gona da iri

Kungiyar Tsaro ta Yammacin Najeriya (WNSN) da aka sanya wa suna Amotekun (Damisa), don magance matsalar tsaro a yankin ta fara wuce gona da iri.

Fara aikin kungiyar ke da wuya aka fara zarginta da wuce gona da wuce makadi da rawa, inda hakan ke jawo ce-ce-ku-ce a yankin Kudu maso Yamma da kuma kasa baki daya.

Ana zargin kungiyar da fara saka da mummunan zare sakamakon inda ake zargin mambobinta da wuce gona da iri, kisan kai, da ta da hankalin jama’ar yankin a lokuta da dama musamman a Jihar Oyo.

Wannan ya sa mutane yankin Yamma da dama ciki har da Farfesa Wole Soyinka suka fara kuka da salon aikin ’yan Amotekun din, sheka guda kacal da aka kafa ta ranar 9 ga Janairun 2020 a Ibadan, Jihar Oyo kuma ita ce kungiyar tsaro ta farko da wata shiyyar siyasar Najeriya ta kafa a tarihin kasar nan.

Ta’asara jami’an Amotekun

Misali a ranar 19 ga Disamban bara, an zargi mambobin Amotekun da kashe mutum biyu a yankin Isale Osi a Jihar Oyo.

Kuma kwana guda da aukuwar hakan aka sake zargin ’yan Amotekun da kisan wani dalibi da ke karatun digiri a ajin karshe a Jami’ar Ibadan.

’Yan Amotekun din sun zargi dalibin mai suna Akolade Gbadebo da zamowa dan fashi kuma dan kungiyar asiri, zargin da Kungiyar Dalibai ta Najeriya (NANS) ta musanta, inda ta ce sun kashe shi ne lokacin da aka gayyato su su buda hanyar da wadansu dalibai suka yi wa shinge.

Sai dai Kwamandan Amotekun na Jihar, Kanar Olayinka Olayanju (mai ritaya) ya musanta zargin.

Sannan a ranar Asabar 2 ga Janairun bana, an zargi ’yan Amotekun da harbin wani dan sanda mai suna Fatai Yekini yayin da suka je Unguwar Sanga da ke garin Oyo lokacin wani biki.

Kanar Olayinka Olayanju ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce, ’yan sanda ne suka gayyaci ’yan Amotekun su taya su tarwatsa bikin, kuma a kokarin haka ne bindiga ta tashi bisa kuskure ta samu dan sandan a cinya.

Harin da ake zargin ’ya’yan kungiyar ta Amotekun da kai wa wasu rugagen Fulani da ke yankin Okebi a Karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa a Jihar Oyo a ranar Asabar da ta gabata shi ne zargin wuce gona da iri mafi muni da aka yi wa ’ya’yan kungiyar.

 An zarge su da kashe Fulani uku, wanda haka ya jawo hankalin jama’a suka fara kokawa da wuce iyakar da ake zargin jami’an na Amotekun da aikatawa.

Aminiya ta samu labarin cewa a harin Amotekun a rugagen Fulanin, ana zargin sun kashe wani dattijo da ’ya’yansa biyu da wadansu da suka rasu a asibiti baya ga wadanda suka samu munanan raunuka.

A sanarwar da Amotekun ta fitar bayan samamen da ta kai a rugagen Fulanin ta ce ta kai harin ne tare da hadin gwiwar Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a wani yunkuri na kawar da masu garkuwa da mutane da suka addabi yankin.

A zantawar da Aminiya ta yi da Shugaban Kungiyar Miyyati Allah ta Jihar Oyo, Alhaji Abubakar Jiji, ya ce duk da cewa da mambobin kungiyar da na jami’an tsaro aka shirya za a kai samame a yankin, sai dai lokacin kai samamen ba a tafi da su ba. Maimakon haka ’yan Amotekun sun zame ne suka je suka yi ta’asarsu.

“Lura da matsalar tsaro da ke addabar yankin namu a Jihar Oyo, mahukunta da jami’an tsaro sun nemi hadin kanmu kan yadda za a kawo karshen matsalar, hakan ya sa muka yi zama a hedikwatar ’yan sandan Jihar Oyo karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan sanda, inda mu shugabannin Kungiyar Miyyeti Allah da na Amotekun da na sauran hukumomin tsaro aka shirya za a yi sintirin hadin gwiwa don kawo karshen matsalar garkuwa da mutane da ta addabi ’yankin.

“Bayan kammala taron aka sa ranar da za a yi aikin, mun shirya ’yan sintirinmu na BGN mun tara su a ranar Juma’ar da ta gabata, muna jiran gari ya waye mu hadu da na Amotekun mu kama aiki, kwatsam sai muka ji labarin ’yan Amotekun sun zame jiki da misalin karfe 2:00 na dare sun kai farmaki.

“Wannan samame da suka yi, shi ne ya yi sanadiyyar kashe wadancan Fulani makiyaya, kuma a gidajensu aka cim musu ba a daji ba.

“Mutum na farko da suka fara kashewa datijjo ne mai kimanin shekara 75 wanda ya wuce shekara 45 a yankin.

“An kashe shi tare da ’ya’yansa maza biyu a safiyar Asabar ranar da yake shirin bikin auren wadansu daga cikin ’ya’yansa.

“Lallai wannan abu bai yi mana dadi ba, mun yi tir da shi muna kuma fata ’yan sanda za su yi bincike kan lamarin,” inji shi.

Dole Amotekun su rika kiyaye hakkin jama’a

Sarkin Fulanin Jihar Oyo, Alhaji Saliu Abdulkadir, ya ce mutanensa ba sa adawa da Amotekun, amma wajibi ne su rika bin doka wajen gudanar da ayyukansu tare da kiyaye hakkin jama’a.

Ya ce, abin da ya faru ranar Asabar inda aka kashe fitaccen Bafullace Alhaji Usman Okebi da ’ya’yansa biyu, hari ne a kan Fulanin da ba su ci ba, ba su sha ba.

“Sun ce masu garkuwa da mutane ne, amma a gidajensu aka iske su. Wannan mutum yana shirye-shiryen auren ’ya’yansa a ranar aka kashe shi,” inji shi.

Sojoji sun Fulani makiyaya 47

Sai dai bayan kashe wadannan Fulani a ranar Asabar wanda hakan ya jawo suka da ce-ce-ku-ce, washegari Lahadi sai ga labarin da ke cewa sojoji sun kama wadansu Fulani makiyaya 47 a Jihar Oyo a samamen da suka kai a yankin Tapa/Igangan a Karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa.

Bayanai sun ce sojojin sun ce sun kama Fulani makiyayan ne lokacin da suke yin yunkurin daukar fansa kan kashe musu ’yan uwa da ’yan Amotekun suka yi a yankin.

Darakta Janar na Operation Burst da suka kama Fulanin, Kanar Oladipo Ajibola (mai ritaya) ya tabbatar da kamen inda ya ce sun mika wadanda ake zargin ga ’yan sanda.

Kakakin ’Yan sandan Jihar, Olugbenga Fadeyi, ya ce makiyayan da aka kama an tura su sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar (CID) da ke Iyaganku, Ibadan.

“An kama wadansu Fulani makiyaya kuma yanzu haka suna sashin CID a Iyaganku a Ibadan.

“Fulani makiyayan sun ce an kama su ne a lokacin da suke farautar masu garkuwa da mutane wadanda suke dab da karbar kudin fansa daga dangin wadanda suka yi garkuwa da shi.

“Ana bincike don gano gaskiyar lamarin,” inji shi.

Kage ake yi wa Fulani

Sai dai Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Jihar Oyo, Alhaji Abubakar Jiji ya musanta cewa Fulanin da aka kama suna shirin daukar fansa ne.

Ya ce “Wani abin takaici shi ne bayan ’yan Amotekun sun gama aika-aikarsu an kuma samun labarin masu garkuwa da mutane a yankin Igagan, sai ’yan sintirin Kungiyar Miyyeti Allah suka isa wajen domin yin samame.

“Amma sai wani Sarkin Fulani ya tsegunta wa sojoji inda suka sanya shinge a yankin suka tsare ’yan sintirin kuma ya kira DPO din ’yan sandan yankin suka kama ’yan sintirin Miyyati Allah 46.

“Yanzu haka da nake magana da kai suna hannun ’yan sanda sai dai muna kokarin ganin an sake so bayan bincike ya tabbatar da ba masu laifi ba ne.”

Yadda ’yan Amotekun suka kashe mana uba da ’ya’yansa 2 –Modibbo

A rugagen Fulanin da harin na Amotekun ya rutsa da su Aminiya ta samu labarin an kone gidajen Fulani da dama da rumbunan kayan abincinsu.

Malam Aliyu Modibbo mazaunin rugar kuma da ga wanda aka kashe tare da ’ya’yansa biyu, ya shaida wa Aminiya cewa, ba masu fasakwauri ko masu garkuwa da mutane ’yan Amotekun suka kashe ba, sun kashe daya daga cikin dattawa kuma limami ne da ’ya’yansa biyu.

“Mutumin da aka kashe, Alhaji Usman Okebi uba yake gare ni, kuma malaminmu ne, yadda abin ya faru shi ne ’yan Amotekun sun shigo kauyen suna harbe-harbe, ko da mutanenmu suka gan su sai suka yi ta gudun tsira, a haka suka harbi wani a kafa.

“Da harbin ya lafa, sai Alhaji Usman ya dauki wanda ’yan Amotekun suka harba a kafa, ya dora shi a kan babur da taimakon ‘ya’yansa maza biyu suka nufi asibiti.

“A hanyarsu ce suka iske ‘yan Amotekun inda suka bude musu wuta, suka kashe tsohon da ’ya’yansa biyu suka karasa kashe wanda ake kokarin ceton ransa.

“Wannan ne gaskiyar abin da ya faru, baya ga su akwai wadanda aka jikkata da dama sun kuma kone gidaje da dama na Fulani,” inji shi.

Umar Salihu Sarki, Shugaban Kungiyar Jamunatil Fulbe ta Fulani makiyaya ’yan kasar Yarbawa, ya shaida wa Aminiya cewa, baya ga limamin da ‘ya’yansa biyu da ’yan Amotekun suka kashe da wanda suka harba da farko suka karasa shi, akwai mutum guda da ya cika a asibiti a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce akwai karin mutum guda da ke kwance a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Abeokuta.

Da Aminiya ta tuntubi Kwamandan Amotekun a Jihar Oyo, Kanar Olayinka Olayanju (mai ritaya), ya ce, babu wani kisa da ’yan Amotekun suka yi a jihar.

“Ni ban san inda aka ce ’yan Amotekun sun kashe wani ba,” inji shi.

Amma da Aminiya ta matsa wa Kwamandan da tambayoyi sai ya kashe wayarsa, daga nan bai sake daga wayar ba, bai kuma maido da amsar sakon waya da wakilinmu ya tura masa kan lamarin ba.

’Yan sanda na kuka da Amotekun

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo wadda ta ce tana bincike kan lamarin, ita ma ta koka kan yadda jami’an Amotekun suke gudanar da ayyukansu a jihar.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Chris Enwonwu ya fadi a wata sanarwa cewa ’yan Amotekun na kai musu mutanen da suka yi wa mugun rauni ta yadda ba za su iya tsare su ba.

Ya kawo misali da abin da ya faru da wani mai suna Alhaji Umaru Salihu da jami’an Amotekun da suka mamayi gidansa suka karbe masa Naira dubu 350 da wasu kudin matansa, suka harbi dansa, kafin su kai shi ga ’yan sanda inda a karshe ya cika a asibiti.

Kamar yadda Kakakin Rundunar Olugbenga Fadeyi ya ruwaito shi a wata sanarwa.

Amotekun za ta fara aiki a Ogun babu jami’anta a Legas

A watan na na Janairu ne Amotekun za ta fara aiki a Jihar Ogun, kamar yadda Gwamna Jihar Dapo Abiodun ya fadi a jawabinsa na sabuwar shekara.

Kuma ya ce tsohon dan sanda ne za a nada a matsayin kwamandan kungiyar wanda akalla ya taba zama kwamshina.

Sai dai har yanzu babu tabbas kan ranar fara aikin Amotekun a Jihar Legas domin har zuwa hada wannan rahoto ba a dauki kowa aiki da sunan Amotekun din ba.

‘Akwai ka’idojin hana su wuce gona da iri’

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Osun, Tunde Olatunji ya ce jami’an Amotekun za su iya daukar bindigogi kamar yadda dokar da ta kafa su ta nuna.

Amma suna da ka’idojin da za su hana su wuce gona da iri wajen amfani da bindigogin.

Shi kuwa Kwamandan Amotekun na Jihar Osun Cif Amitolu Shittu ya ce kungiyar ta samu nasarori da dama wajen kwato dukiyar da aka sace lokacin boren #EndSARS.

Shi ma Kwamandan Amotekun na Jihar Ekiti, Birgediya Joe Komolafe (mai ritaya) ya ce kungiyar ta samu nasarar magance miyagun ayyuka a jihar.

Ya bukaci jama’a su rika kai musu bayanai a kan lokaci don dakile aukuwar miyagun ayyukan a jihar.

Doka ta yarda mu dauki bindigogi –Amotekun

Kwamandan Amotekun na Jihar Ondo, Cif Adetunji Adeleye ya ce duk da cewa kungiyar na aiki ne da sauran hukumomin tsaro, dokar jihar ta 2020 ta amince jami’ansu su dauki bindigogi.

Ya ce amma an horar da jami’ansa yadda ya kamata kan yadda za su sarrafa wadannan makamai a lokacin da suke aikin da doka ta yarda da shi.