✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ya kamata rayuwar Kirista ta kasance (5)

Yawancin lokaci rashin gane ayyukan Shaidan ne kawai yakan sa mutane su yi gaba da junansu. Yesu Kiristi na koya mana yadda za mu iya…

Yawancin lokaci rashin gane ayyukan Shaidan ne kawai yakan sa mutane su yi gaba da junansu. Yesu Kiristi na koya mana yadda za mu iya gane juna, mu kuma nuna wa mutane hanya madaidaiciya da jama’a za su iya bi su ci nasara bisa kowace hilar Iblis; amma babu shakka sai in mutum ya riga ya ba da gaskiya da shirin ceton dan Adam daga bautar zunubi. Idan mutane masu bin Yesu Kiristi sun gane cewa; Iblis ne yake izza mutane su wulakanta su, ba za su ji haushin irin wadannan mutane ba; shi ya sa Yesu Kiristi ya ce mu yi musu addu’a domin idonsu ya budu su iya gani ko wane irin ruhu ne yake aiki a jikinsu. kauna ce kadai za ta iya sa mu yin addu’a dominsu.
Maganar Ubangiji Allah ta ci gaba da koya mana cewa; “Wanda ya mare ka a wannan kumatu ka juya masa dayan kuma; wanda ya amshe maka mayafi kada ka hana masa riga kuma.”(Luka:6:29). To ga wata sabuwa kuma a nan; wannan irin marin, ba wai domin ka yi wani laifi ba ne a’a; ka tuna akwai mutane da yawa a wannan zamani wadanda suka cika neman tsokana, ba lallai ne a ce ka shiga cikin sha’aninsu ba, su za su kawo kansu. A yau muna ganin irin wannan yana aukuwa kusan kowane lokaci. Masu bin Yesu Kiristi da dama suna fuskantar irin wannan kalubale; kana cikin gidanka, ko kuwa cikin masujada, ba zato ba tsammani sai ka ga mutane sun auko maka kuma idan ba ka yi sa’a ba; har kashe za su yi, to; a cikin irin wannan hali mene ne ya kamata kai mai bin Yesu Kiristi ka yi? Amsar daya ce; ka yi musu addu’a!! A yau masu bi da yawa suna so idan da zai yiwu, a samu a canja wannan aya domin ana dauke da zuciyar ramako, amma gaskiyar kuma ita ce – Maganar Allah babu wanda ya isa ya canja, wannan kalmar ta zauna har abada kuma ba ta canjawa. Yesu Kiristi cikin koyarwarsa, ya ce idan har wani ya mare ka a wannan kumatu sai ka juya masa dayan, wannan ba abu ne mai sauki ba ko kadan, amma idan mun rigaya mun san shi Yesu Kiristi Ubangijinmu ne, takan zama da sauki ta wurin ikon ruhunsa mai tsarki ma iya yin hakuri mu kuma iya jure kowace irin wahala. Yesu Kiristi ya riga ya yi magana a cikin Littafin Yohanna:16:2: cewa “Za su fitar da ku daga cikin majami’u; eh sa’a tana zuwa inda dukan wanda za ya kashe ku, za ya zaci yana yi wa Allah hidima.” Ba bakon abu ba ne ga masu bin Yesu Kiristi a wannan kasa, mun sha dandana irin wannan wahala sau da dama. Ubangiji Allah bai bar mu cikin duhu ba; Ya fada mana abin da zai faru da mu tun kafin su soma faruwa. A yau; wannan nassi ya cika a gabanmu, Yesu Kiristi ya ce sa’a na zuwa inda dukan wanda ya kashe ku, za ya zaci yana yi wa Allah hidima, kuma gaskiya haka yake. Kisan da ake yi wa Kirista a yau, ana yinsa ne a cikin sunan yi wa Allah aiki. Sai mu lura mu kuma tambayi kanmu kamar haka; idan wani ya zo ya kashe dan uwanka a cikin sunan yin aikin Allah, mene ne ya kamata kai ka yi a matsayinka na Kirista? Bisa ga koyarwar Littafi Mai tsarki, bai kamata ka rama mugunta da mugunta ba, ka tuna fa cewa rashin sani ne yakan kawo irin wannan halin keta da ayyukan Iblis. Ka sani cewa a matsayinka na Kirista, abu guda daya da dole ka yi shi ne – ka nuna musu kAUNA. kauna halin Allah ne, idan kana son wani ya san Allah ta wurin rayuwarka, sai ka nuna masa sahihiyar kauna. Hanyoyin nuna irin wannan kauna kuwa sun kunshi yi ma irin wadannan mutane addu’a. Yi musu nagarta, sa musu albarka kada ka la’anci kowa, ka yi addu’a domin Allah Ya bude idonsu su gane irin duhun da suke ciki, haka ne haske zai ci nasara bisa duhu.
Me ya sa za mu nuna sahihiyar kauna ga irin wadannan mutane? Watakila shi ne irin tunanin da ke shigowa cikin zuciyarka a yanzu, dalilin daya ne domin kana so su samu rai madauwami. Kodayake Allahn da muke bautawa ba Ya son zunubi amma Yana kaunar masu zunubi; shi ya sa Ya aiko da Yesu Kiristi domin ya mutu sabili da dukan duniya. Dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kuma za ya tsira. Idan har mun iya jure wahalar wannan dan lokaci to, babu shakka za mu ci nasara.
 Sai mu zama masu lura a kullum, domin mu iya bayyana halin Kiristi a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, haka haskenmu zai haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanmu masu kyau su kuma girmama Ubangiji Allahnmu Wanda ke cikin sama.
Mu ci gaba da addu’a muna rokon Allah Ya ci gaba da tsare mu daga masifun da ke kewaye da mu, amin.