✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ya kamata rayuwar Kirista ta kasance (3)

Irin wadannan mutane ne Ubangiji Allah Yake cewa mu yi musu nagarta. A cikin rayuwar yau da kullum, kowane mai ba da gaskiya ga Yesu…

Irin wadannan mutane ne Ubangiji Allah Yake cewa mu yi musu nagarta. A cikin rayuwar yau da kullum, kowane mai ba da gaskiya ga Yesu Kiristi; dole ya gane cewa ba ya da makiyi sai shi Iblis da kansa, Shaidan shi kadai ne makiyi, kodayake yana yin amfani da mutane domin ya aikata nufinsa, amma gaskiyar ita ce ba mutumin da Shaidan ya yi amfani da shi; shi ne makiyinka ba, ya kamata mu gane cewa, yawanciin lokaci, mutum ba ya iya ganinsa Shaidan din da yana bayan ayyukan dukan makiya, domin mun cikin wannan jiki na mutuntaka; abin da muke gani mutumin da yake yin miyagun ayyukan ne ba Shaidan ba, bari mu sani da cewa ruhun da yake aiki a cikin kowane makiyi ba Ruhun Allah ba ne amma ruhun Iblis ne. Shi ya sa bai kamata mai bin Yesu Kiristi ya rike mutum cikin zuciiyarsa domin ya yi masa mugunta ba. Idan har muna so mu gamsar da Ubangiji Allah, sai mu bar Ruhunsa ya bishe mu cikin tafiyarmu da sauran mutane.
Muna cikin zamani mai wuyan gaske wanda mutane da yawa za su so su ci zarafinka; amma duk da wannan, abu guda da zai taimaka mu iya nuna sahihiyar kauna har ga wanda idan ya samu zarafi zai iya hallakar da mu shi ne sanin ikon alherin Allah da yake cikin kowane dayanmu ta wurin ikon Ruhunsa. Alherin Allah ne zai sa mu iya yin abubuwan da zai yi wuya a yi su a haka nan kawai.
Nagarta: Yin abin kirki ne ga wani, aikata wani abu mai kyau ko yin alheri ga wani; wannan na da sauki sosai idan za ka yi wa masoyinka ne ko kuma ga wanda kake kauna. Za ka iya sadaukar da komai dominsa, wannan kowa zai iya aikatawa. Amma ga mai bin Yesu Kiristi; daya daga cikin abin da zai bambanta ka da sauran mutane shi ne, ka iya aikata wannan alherin ga wanda ya riga ya nuna maka kiyayya, ko kuwa wanda ka san watakila ta wurin ayyukansa cewa tunaninsa zuwa gare ka a kullum tunanin mugunta ne ba na alheri ba ko kadan. Mutane da yawa za su ce da kai mai wauta, mara tunani, mai yiwuwa ne mutane da yawa za su zage ka hakan, su ce, kai wani irin mutum ne? Kada ka damu da mutane irin wadannan, suna so ne su kawar da kai daga bin tafarkin Allah. Sai mu lura da shawara ko ra’ayin mutane game da umarnin da Allah Ya rigaya Ya bayar, domin zai zama babban kuskure ne ga kowane Mai bin Yesu Kiristi.
Idan ka dauki mutum a matsayin magabcinka, sai ka sani ka saba wa umarnin Allah, kuma rana tana zuwa da dole za ka ka fuskanci Allah a lokacin shari’arSa. Kuma ba ka da hujja ko kadan kan rashin yin biyayya ga maganarSa. A lokacin tsanani kamar wadda muke ciki a yanzu, kada mu manta cewa kodayake muna cikin wannan duniya, amma mu ba na duniya ba ne. Wata rana za mu koma wurin Ubangijinmu da Allahnmu. Bari mu jure kowace irin wahala na dan lokaci. A cikin irin wannan hali, akwai abu guda daya wanda kowane Mai bin Yesu Kiristi ya kamata ya dukufa ga yi – ADDU”A. Addu’a ita ce kadai makaminmu. Ba yin addu’a domin “mutum makiyinka” ya mutu ba, amma domin Allah cikin alherinSa Ya bude masa ido ya ga Shaidan da yake bayan halayensa ya kuma juyo.
Yayin da muke ci gaba da wannan koyarwa; Allah cikin ikonSa Yana bude mana ido domin mu gane irin rayuwar da ya kamata mu yi cikin wannan duniya da take cike da masu mugunta. Asirin rayuwa mai albarka, rayuwa irin wadda Allah da kanSa zai gamsu da ita, mu da kanmu ma mu sami gamsuwa. Sau da dama masu bin Yesu Kiristi sukan manta da ko wane ne su, wadansu suna mantawa cewa akwai bambanci tsakaninsu da sauran jama’a da suke kewaye da su. Maganar Allah na koya mana cewa “Idan fa kowane mutum yana cikin Kiristi, Sabon Halitta ne; tsofaffin al’amura sun shude ga kuwa sun zama sababbi.” (2Korinthiyawa 5:17). Duk wanda ya rigaya ya ba da gaskiya da hadayar da Yesu ya yi a bisa kan gicciye, to babu shakka yana da sabon rai na har abada cikin Kiristi Yesu, Allah ta wurin ikon Ruhunsa Mai tsarki Ya canja shi da duk tunaninsa.
Ubangiji Allah Ya san irin kalubalen da masu bin sa za su fuskanta, shi ya sa Ya soma shirya zuciyarsu game da irin mutanen da za su fuskanta a yau da kullum; Ya kuma ba su basirar rayuwa a lokacin da suka samu kansu cikin kowane hali. Koyarwar Yesu Kiristi ba kamar ta sauran Annabawa ba ne, yayin da cikin dokoki da shari’ar Musa; mun ga yadda Allah Ya ba da izini idan ka yi wa wani laifi, za a iya hukunta ka gwargwadon laifin da ka aikata. Amma a cikin dukan wannan; Allah Yana hangen zuwan Yesu Kiristi ne a nan gaba. Da Yesu Kiristi ya bayyana, sai mu ka ga cikakkiyar koyarwa da kuma umarnin da kowane mai bin Yesu Kiristi zai lura da su.

Ku albarkaci masu zaginku:
“Ku albarkaci masu zaginku; wadanda suke wulakanta ku, ku yi musu addu’a.” (Luka 6:28). Abin da nake so mu lura da shi ne, shi ne wannan kalma zagi! Yadda aka yi amfani da wannan kalma a nan, ba kawai na nufin ashar, ko kuwa fadin wadansu kalmomin da ba su da dadin ji ba ne; a wannan wurin, na nufin la’ana ne. La’ana dai fatar wani abu mummuna ya faru da wani, fatar wani bala’i ne ya zo bisa ga wani, ba fatar alheri ba ne koda wasa.