✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ya kamata rayuwar Kirista ta kasance (2)

Duk lokacin da ka fuskanci damuwa irin wannan; ka tuna da wannan koyarwa, asirin cin nasara bisa kowane magabci shi ne – nuna masa sahihiyar…

Duk lokacin da ka fuskanci damuwa irin wannan; ka tuna da wannan koyarwa, asirin cin nasara bisa kowane magabci shi ne – nuna masa sahihiyar kauna da kuma yin addu’a dominsa. Addu’a; ba domin su mutu ba kamar yadda na san wadansu mutane ke yi, amma domin su samu alherin Allah; kada mu yi kuskuren la’anta wani domin ganin cewa ya yi mana ba daidai ba. Makaman yakinmu na masu bi su ne – kAUNA da ADDU’A. Zai zama kuskure ga kowane mai bin Yesu Kiristi ya dauki wadansu makamai. Bindiga ko adda ko wuka da makamantansu, ba kayan fadan masu bi ba ne, yakin kowane cikakken mai bi a kan gwiwarsa yake yi cikin addu’a a gaban Allah Masanin komai duka. Lallai babu shakka zai zama da wahala ga wanda ba shi da Ruhun Allah a cikinsa, ga mai bin Yesu Kiristi; wannan ita ce asirin cin nasara bisa kowane mutum, mai gaba da kai a kowace fanni. Akwai dalilin da Yesu Kiristi ya koyar da almajiransa haka, ya ce “Domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama: gama Yakan sa rana taSa ta fito wa miyagu da nagargaru, Yakan aiko da ruwa bisa masu adalci da marasa adalci.”
Idan har muna so mu bi gurbin Ubangijinmu Yesu Kiristi, babu wata hanya kuma da za mu bi sai dai wannan da ya koya mana. A cikin rayuwar yau da kullum, sai mu tuna cewa mu ne hasken wannan duniya, bari mu bar wannan hasken ya haskaka. Ubangiji Ya taimake mu iya tafiya da ta cancanci kiranmu.
Mun soma wannan koyarwar ce daga cikin Littafin Luka 6: 27 – 38 wadda nake son mu sake karantawa: “Amma ku masu ji, ina ce muku, ku yi kaunar magabtanku, ku yi wa makiyanku nagarta, ku albarkaci masu zarginku; wadanda suke wulakanta ku, ku yi masu addu’a. Wanda ya mare ka a wannan kumatu, ka juya masa wannan kuma; wanda ya amshe maka mayafi kada ka hana masa riga kuma. Ka bayar ga kowane mai rokonka; wanda ya kwace maka dukiyarka kuma kada ka bide su a gare shi. Kuma kamar yadda kuke so mutane su yi muku, ku yi musu haka nan kuma. Idan kuwa kuna kaunar masu kaunarku; wane abin godiya ke gare ku? Gama da masu zunubi suna kaunar masu kaunansu. Idan kuma kuna yin nagarta ga wadanda suke yi muku nagarta, wane abin godiya ke gare ku? Gama har da masu zunubi suna yin wannan. Idan kuwa kuna ba da rance ga wadanda kuke sa zuciya za ku samu a gare su, wane abin godiya ke gare ku? Har da masu zunubi suna ba da rance ga masu zunubi, domin su samu kuma misalin abin da suka bayar. Amma ku yi kaunar magabtanku ku yi musu nagarta, ku ba da rance, kada ku fidda zuciya dadai; ladarku kuwa mai girma ce za ku zama ’ya’yan Madaukaki, gama Shi Mai alheri ne ga marasa godiya da miyagu. Ku zama masu jinkai kamar yadda Ubanku Mai jinkai ne. Kada ku zartar, ku kuma ba za a zartar muku ba: kada ku kayar, ku kuwa ba za a kashe ku ba: ku kwance, za a kwance ku kuma: ku bayar, za a ba ku mudu mai kyau, dankararre, girgizajje, mai zuba, za su bayar cikin kirjinku. Gama da mudun da kuke aunawa da shi za a auna muku.”  
Ku yi wa makiyanku nagarta:
“Amma ku masu ji, ina ce muku, ku yi kauar magabtanku, ku yi wa makiyanku nagarta. Ku albarkaci masu zarginku, wadanda suke wulakanta ku, ku yi musu addu’a.”
Bari mu sake duba wannan maganar da Yesu Kiristi ya yi; cewa “Amma ku masu ji, ina ce muku,” Ubangiji Allah Ya sani cewa wannan koyarwar ba mai sauki ba ce ko kadan, kuma ba kowane mutum ba ne zai ji irin wannan, shi ya sa ya ce “amma ku masu ji;” ba abu mai sauki ba ne ko kadan mutum ya yi wa makiyansa nagarta, bari mu duba ko wane ne makiyi. Makiyi, mutum ne wanda idan ya yi tunaninka cikin zuciyarsa, kada ka yi shakkar komai – tunanin mugunta ne yake yi, makiyinka a kullum yana neman hanyar da zai cuce ka ne. Makiyinka, mutum ne wanda idan ya samu zarafi zai iya kashe ka domin dama ba ya son ganin ka: Maganar Allah na koya mana cewa “Dukan wanda ya ki dan uwansa mai kisan kai ne: kun sani babu mai kisan kai wanda shi ke da rai na har abada cikinsa zaune.” Daga wannan wurin da muka karanta, mun ga cewa makiyi mai kisan kai ne, kuma irin wannan mutum ne Allah Yake son dukan masu bi su iya yi masa nagarta; gaskiyar ita ce wannan ba abu mai sauki ba ne ko kadan.
Bari mu sa ke duba maganar Allah domin mu samu cikakken ganewa, a cikin Littafin Misalai: 26: 24 – 26; maganar Allah na cewa “Mai kiyayya yakan yi kinibibi da bakinsa. Amma rikici yake ajiyewa a zuciyarsa. Sa’anda yana magana mai dadi, kada ka ba shi gaskiya: gama akwai abin kyama guda bakwai ne a cinkin zuciya tasa.”  
Irin wadannan mutane ne Ubangiji Allah Yake cewa mu yi musu nagarta. A cikin rayuwar yau da kullum, kowane mai bada gaskiya ga Yesu Kiristi; dole ya gane cewa ba ya da makiyi sai shi Iblis da kansa, Shaidan shi kadai ne makiyi, kodayake yana yin amfani da mutane domin ya aikata nufinsa, amma gaskiyar ita ce ba mutumin da Shaidan ya yi amfani da shi; shi ne makiyinka ba, ya kamata mu gane cewa, yawancin lokaci, mutum ba ya iya ganin shi Shaidan din da yana bayan ayyukan dukan makiya, domin mun cikin wannan jiki ta mutuntaka; abin da muke gani mutumin da yake yin miyagun ayyukan ne ba Shaidan ba, bari mu sani da cewa ruhun da yake aiki a cikin kowane makiyi ba Ruhun Allah ba ne amma ruhun Iblis ne, shi ya sa bai kamata mai bin Yesu Kiristi ya rike mutum cikin zuciyarsa domin ya yi masa mugunta ba. Idan har muna so mu gamsar da Ubangiji Allah, sai mu bar Ruhunsa ya bishe mu cikin tafiyarmu da sauran mutane.