✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda wasu ’yan kabilar Ibo ke shirin Babbar Sallah

Yadda ake bikin sallah a gidan Babban Limamin Imo, Shaikh Suleiman Yusuf Njoku

Kamar sauran Musulmai a fadin duniya, iyalan Alhaji Suleiman Njokwu, na shirye-shiryen bikin Babba Sallah.

A idin babbar sallah ana bukatar Musulmai masu hali su yanka dabbar layya.

A matsayinsa na Babban Limamin Jihar Imo, Imam Suleiman Njokwu na da karin nauyi a kansa n ilmantarwa da kuma fahimtar da Musulmi a fadin  jihar wanda kuma ke bukatar sa ya yi kyakkyawan shiri.

Sai dai bana idin ya sha bamban, domin maimakon yadda aka saba yin sallar a filin idi da ke Nekede ko Amausa, bana za a yi  sallar ce a cikin masallatai saboda annobar coronavirus.

“Za mu yi sallar a cikin masallatai, bisa tsarin dokar COVID-19, musamman na bayar da tazara da kuma sanya takunkumi”, inji shi.

Bukukuwan da aka yi a baya

Amma a baya ba haka aka saba yin sallar Idin ba.

“Lokacin idi akan yi shagulgula ne da kuma kawa”, akan yi “bukukuwa da ciye-ciye da tande-tande iri-iri har a raba wa mutane a kuma ziyarci abokan arziki.

“Yanzu wannan ya kau. Dole mu san yadda za mu yi bikin ta yadda ba za mu saba dokar COVID-19 ba.

Wannan shekarar ba za a yi shagulgula ba.

A matsayinsa na limami

Kasancewrsa mai mata daya da ‘ya’ya uku, yawan iyalansa bai kai na mahaifinsa ba, Alhaji Yusuf Njoku, mai mata uku da ‘ya’ya 14, wanda ya rasu a 1995.

Mahaifin nasa ya zauna a Kano inda ya auri matarsa ta farko, wadda Bafulatana ce.

Mahaifiyar Imam Suleiman Njoku, ‘yar asalin Umuevu Umuokrika da ke Mbaise a Jihar ta Imo ita ce matar mahaifinsa ta biyu.

A shekarar da ta gabata ne Majalisar Musulmai ta Jihar Imo ta nada Babban Limamin Jihar, bayan rasuwar Alhaji Dauda Onyeagocha.

Bayan jagorancin sallolin Juma’a da na ido, Imam Njoku kan shirya liyafar sallah a gida.

Bikin sallah a cikin gida

Bayan hawan idi Imam Njoku da iyalansa kan koma gida ne tare da ‘yan uwa inda suke shakatawa da kuma karbar bakuncin masu kawo musu ziyara.

Amma ya ce, “hatta Shugaba Buhari ya hana [mutane] su kai masa ziyara a Aso Rock a lokacin [karamar Sallah].

“Saboda haka sai mu yi bikin ba tare da yin taro ba, saboda yanayin da muke ciki”, inji shi.

Ya ce, “A matsayinmu na iyali, insha Allahu za mu yi bikin daidai da dokar Allah. Manufar ita ce nuna farin ciki da gode wa Allah da Ya raya mu zuwa wannan lokaci”.